Lokacin mafi falala na sallar wutiri
Idan mutum zai iya tashi a ƙarshen dare yayi sallar wutiri to jinkirta ta shi yafi, amma idan bazai iya tashi ba to yayi shi a farkon dare shi yafi.
Jabir ɗan Abdullahi Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
مَن خافَ أنْ لا يقومَ مِن آخِرِ اللَّيلِ فلْيُوترْ أوَّلَه، ومَن طَمِعَ أن يقومَ آخِرَه فلْيُوترْ آخرَ اللَّيلِ؛ فإنَّ صلاةَ آخِرِ الليلِ مشهودةٌ، وذلك أفضلُ
Wanda yaji tsoron ba zai tashi a ƙarshen dare ba yayi wutiri a farkon sa, wanda yake kwaɗayin zai iya tashi a ƙarshen sa to yayi wutiri a ƙarshen dare. Domin Sallah a ƙarshen dare Mala’iku suna halartar ta, shi yafi falala,
Sahihu Muslim: 755
Wannan hadisi yana nuna falalar jinkirta Sallar Wutiri zuwa ƙarshen dare ga wanda zai iya tashi a ƙarshen daren, amma idan mutum bazai iya tashi ba sai yayi a farkon dare.
Adadin raka’oin sa:
Wutiri raka’a ɗaya ne wanda ake rabe shi da na bayan sa. Ma’ana bayan an sallame daga shafa’i sai ayi wutiri. Misalin wanda zaiyi raka’a uku sai yayi raka’a biyu ya sallame sai yayi raka’a ɗaya a ƙarshe sai ya sallame, wannan shine wutirin sa.
Ibnu Umar Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito wani mutum ya tambayi Annabi game da Sallar dare
أنَّ رجلًا سألَ رسولَ اللهِ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم عن صلاةِ اللَّيلِ، فقال رسولُ اللهِ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم: صلاةُ اللَّيلِ مَثْنَى مَثنَى، فإذا خشِي أحدُكم الصبحَ صَلَّى ركعةً واحدًة، تُوتِرُ له ما قدْ صلَّى
Wani Mutum ya tambayi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da Sallar dare sai yace masa Sallar dare raka’oi biyu biyu ne, idan ɗaya daga cikin ku yaji tsoron Asubahi zai riske shi sai yayi sallah raka’a ɗaya ta zamto masa wutirin abinda ya sallata a baya.
Sahihul Bukhari: 990. Sahihu Muslim: 749
Hakanan Ibnu Umar Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
الوترُ ركعةٌ من آخِرِ اللَّيلِ
Wutiri Raka’a ɗaya ce a ƙarshen dare
Sahihu Muslim: 752
Abinda ake karanta wa acikin wutiri
Sunnah ce mututm ya karan ta Suratul A’ala da Suratul Kafirun a shafa’i, sai ya karanta Suratul Ikhlas a raka’ar Wutiri.
Abdullahi bin Abbas Allah ya ƙara yarda dashi yace:
Annabi ya kasance yana wutiri da raka’oi uku, yana karanta Suratul A’ala a raka’a ta farko, ya karanta Suratul Kafirun a Raka’a ta biyu ya karanta Suratul ikhlas a raka’a ta ƙarshe
Tirmidhi: 462. Annasa’i: 1702
Sannan Bayan Mutum ya kammala sallar wutiri anaso yace
Subhanal Malikil Quddus sau uku, a na ukun ya ɗaga Muryar sa.
Abu Dawud: 1403. Annasa’i: 1699. Ahmad: 21180
Domin sanar damu wani kuskure ku tuntuɓe mu ta WhatsApp