Jarabawar Rayuwa(1): Yana daga cikin Jarabawar rayuwa awanni 24 su wuce ba tare da Mutum ya karanta wani abu na Alqur’ani ba koma bayan wanda yake karantawa acikin salloli 5.

Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

AlQur’ani mai girma Maganar Allah ne, wanda ya sauƙar wa Manzon sa Annabi Muhammad Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda ya ƙunshi dukkan alheri na duniya da lahira.

Duk abinda kakeso na alheri Alƙur’ani ya ƙunsa.

Shiyasa akeso Musulmi ya lazimce shi, ya karanta shi da Tadabburin Ayoyin sa.

Wanda Ya sauƙar da wannan Alƙur’ani shi ya haliccemu kuma yasan abinda ya dace damu.

Ƙaddara wani Injiniya ne ya ƙirƙiri wata Na’ura mai wuya sarrafa wa da kuma hatsari, sai ya rubuta mata Manual(yadda za’ayi aiki da ita) sai ka sayi na’urar ka ɗauki wannan takarda da yake ciki kana karanta wa domin ka fahimci yadda zakayi amfani da ita sai wani yazo yace maka ai kana ɓata lokacin ka, kawai kayi amfani dashi yadda kaga dama. Wanne zaka bi a matsayin ka na mai hankali? Zaka cigaba da karatun ka ne domin fahimtar yadda zakayi amfani da wannan na’ura, kuma ka kiyaye shi daga ɓaciwa ko kuma zaka ɗauki shawarar sa?

Ina da tabbacin mai hankali zai zaɓi yaci gaba da karanta Manual ɗin domin fahimtar yadda zaiyi amfani da wannan na’ura.

To haka lamarin yake, Duk wanda yabi Alƙur’ani to haƙiƙa yabi Manual da Allah ya sauƙar wa bayi domin su fahimci yadda zasuyi rayuwar su yadda ta dace. Wanda kuma yabi son zuciyar sa haƙiƙa yabi tafarkin marasa hankali.

Wannan Alƙur’ani mai wannan matsayi a rayuwar Mutum bai dace Awanni 24 su wuce a rayuwar mutum ba tare da ya karanta wani ɓangare nashi ba, kuma yayi tadabburin ayoyin sa sai dai idan akwai lalura.

Ko ban kawo falaloli na karanta Alƙur’ani ba ya kamata ga mai Hankali ya riƙi wannan Alƙur’ani hanu bibbiyu, wurin karanta shi da fahimtar Ayoyin sa, domin da shi ne zai fahimci yadda zai gudanar da Rayuwar sa cikin Natsuwa da kwanciyar hankali, ina kuma ga Falaloli masu yawa da masu ƙaranta Alƙur’ani da riƙo dashi suke samu!!!

Allah maɗaukakin sarki yace:

Lallai ne wannan Alƙur’ani yana shiryarwa zuwa ga tafarki mafi daidai ta.

Suratul Isra’i: 9

In kana neman shiriya to kayi riƙo da Alƙur’ani.

Allah ya sake cewa:

Kuma wannan littafi ne mun sauƙar dashi mai cike da albarka, ku bishi.

Suratul An’an: 155

In kana neman Albarkar duniya da Lahira to kayi riƙo da Alƙur’ani mai girma.

Game da Falalan karanta Alƙur’ani:

Abu Umamatal Bahili Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi tsira da amimcin Allah su tabbata a gare shi yace:

Ku karanta Alƙur’ani, domin zaizo ranar Tashin Alƙiyama yana ceton masu karanta shi

Sahihu Muslim: 804

Girman ladan karanta Alƙur’ani

Abdullahi Bin Mas’ud Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi yace:

Duk wanda ya karanta Harafi ɗaya na Littafin Allah yana da Lada, kowani lada ana ninnin ka shi zuwa goma, ba ina cewa (Alif Laam Meem) Harafi ɗaya ba, (Alif) Harafi (Laam) Harafi (Meem) Harafi

Tirmidhi: 2910

Wannan shine irin ladan da makarancin Alƙur’ani yake samu. Duk harafi ɗada da mutum ya karanta yana da Lada goma. Wanda Ya Karanta “Alif laam meem” yana da Lada talatin, ƙaddara ko shafi ɗaya ka karanta Lada nawa kake dashi?

Karanta Alƙur’ani babu asara acikin sa, ko baka iya karanta shi da kyau ba zaka samu lada biyu, ladan karatu da ladan Shan wahalar karanta wa, sai dai a kullum kayi iya ƙoƙarin ka wurin ganin cewa ka koyi karanta Alƙur’ani yadda ya dace a karanta shi.

Aisha Allah ya ƙara mata yarda ta rawaito daga Annabi yace:

Wanda yake karanta Alƙur’ani alhali ya hadda ce shi(gangaran), yana tare da Mala’iku, ɗaukakakku, masu biyayya ga Allah, Wanda kuma yake karanta Alƙur’ani yana bibiyar sa, yana samun wahala wurin karatun yana da lada biyu

Sahihul Bukhari: 4937

Wannan Hadisi yana nuna Muhimmancin Haddace Alƙur’ani, amma idan mutum bai haddace ba kada ya kariya, yayi iya ƙoƙarin sa ya karanta iya iyawarsa, Allah maɗaukaki zai bashi lada.

Ya ɗan’uwa Shin kana ga duka wannan falala ta karanta Alƙur’ani da muka ambata anan, amma a samu awanni 24 su wuce ba tare da ka buɗe Alƙur’ani ba kana ga baka cikin jarabawa ta Rayuwa?

Ya kamata ka tambayi kanka menene dalilin halittar ka wataƙila hakan zai sa kayi tunani ka koma kan Tafarkin da ya dace.

Allah yasa mudace, Allah ya sanya mu cikin ma’abota Alƙur’ani.

Leave a Reply

Scroll to Top