Hukuncin Namiji yayi wa mace dinki da kuma Hukuncin gwada ta domin dinkin

Tambaya: Assalamu alaikum wa rahmatul lah Allah yakawa malan lafiya ameen ya hayyu ya qayyum dan Allah malan me hukuncin namji tela Mai dinki yana gwada mata kuma sannan inza a nunamai kalan dinkin dazaiyi zakaga an’nunamai hoto Mai dauke da mata suna rawa ina hukuncin shi a musulunci.

Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Shimfiɗa:

Shari’ar Musulunci yazo da tsare duk wata kafa da zata kai ga aikata Alfasha. Shiyasa lokacin da Allah yake hani kan zina bai ce kada kuyi zina ba sai yace:

Kada ku kusanci Zina

Suratun-Nisa: 32

Haka nan ya sake faɗa a wata Aya yace:

Kada ku kusanci Alfasha wanda ya bayyana da wanda ya ɓuya.

Suratul-An’am: 151

Duka wa’innan ayoyi suna nuna muhimmancin nesantar alfasha, domin kusantar ta ka iya sa mutum ya faɗa cikin ta.

Haka nan Allah yayi gargaɗi wa muminai maza da mata kan rimtse idanunsu, Yace:

Ka faɗa wa Muminai maza su rimtse idanuwan su sannan su kiyaye farjin su,

Suratun-Nur:30

Ya faɗa wa mata suma yace musu:

Sannan ka faɗa wa Muminai Mata su rimtse idanuwansu, sannan su kiyaye farjin su, sannan kada su bayyana adon su sai dai wanda ya bayyana(Wanda baza’a iya rufe wa ba)

Suratun-Nur:31

Duka wa’innan Ayoyi suna koyar da Al’ummah kauce wa faɗa wa Hatsarin zina.

Amsa:

Babu laifi ga namiji yayi wa mace ɗinki, amma da sharaɗin kauce wa duk wata hanya da ta tsaɓa wa shari’a. Wanda gwada mace yana da cikin.

Baya halatta ga namiji ya taɓa mace wacce ba Muharramar sa ba. Kuma abu ne sananne cewa idan yazo gwada ta dole sai hannun sa ya taɓa jikin ta.

Saboda haka Baya halatta a gare shi ya gwada ta, sai dai idan zai ɗinka mata ba tare da gwadi ba, ko kuma ya sanya wata mace ta gwada ta, kamar matar sa ko ƴar sa.

Game da cewa in za’a nuna masa kalan ɗinkin da zaiyi ana nuna masa video wanda ke ɗauke da mace tana rawa wannan shima haramun ne.

Domin kallon hoton mace wacce ba Muharramar Mutum ba baya halatta. Haka nan Rawa da waƙa shima Haramun Ne.

Saboda haka ya wajaba akan Musulmi yaji tsoron Allah ya rinƙa kula da hanyar neman abincin sa, ya tabbata hanya ce ta Halal. In yayi iya ƙoƙarin sa aka samu wani kuskure kuma to Wannan Allah bazai kama shi dashi ba.

Sannan kuma masu ɗinki su kula da ɗinkin da sukeyi wa mata, musammam budurwaye, kada su yarda su rinƙa yi musu ɗinki da ya tsaɓa wa Shari’ah musamman in suna da yaƙinin zasu rinƙa fita waje da ɗinkin mutane suna gani, domin hakan taimaka musu ne akan tsaɓon Allah, wanda kuma Haramun ne kamar yadda Allah ya yace:

Ku taimaki juna kan ɗa’a wa Allah da kuma taƙawa, kuma kada ku taimaki juna kan tsaɓon Allah da ƙetare iyaka

Suratul Ma’ida: 2

Saboda Haka dole tela Musulmi ya wajaba yayi taka tsan tsan cikin aikin sa, kada ya bari shaiɗan ya rinjaye shi.

Sheikhul Islam Ibnu Taimiyyah Allah yayi masa Rahama yace:

Duk wani tufa wanda zato yafi karkata kan cewa za’ayi amfani dashi ne wurin tsaɓa wa Allah baya halatta a sayar dashi ko a ɗinka shi ga wanda zaiyi amfani dashi wurin tsaɓa wa Allah.

Sharhul Umda: 4/386

A Taƙaice:

Babu laifi na miji ya ɗinka wa mace kaya. Amma dole a kula da haƙƙoƙi Shari’a wurin yin Hakan. Baya Halatta a gareshi ya taɓa jikin ta wurin gwada ta.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top