Hukuncin wanda ya saki Matar sa Cikin Fushi

Tambaya: Menene Hukuncin wanda ya saki matarsa cikin fushi? Sakin yayi ko baiyi ba?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Game da wannan Hukunci Maluma sun raba fushin gida uku.

1. Na farko: Fushi ba mai tsanani ba; wanda ya saki matarsa a yayin da yake fushi amma fushin ba mai tsanani ba to wannan Saki ya auku, an samu Ijma’in Maluma kan haka.

Ibnu Rajab Allah yayi masa Rahama yace:

Abinda yake aukuwa daga Mai fushi, na saki, ko ƴanta bawa, ko rantsuwa ana kama shi da wannan abu da yayi, babu tsaɓani kan haka.Jami’ul Ulumi wal Hikam: 1/375

Sheikh Bin Baz Allah yayi masa Rahama yace:

Hali na Uku: Fushi wanda ba mai tsanani ba, wannan idan mutum yayi saki cikin wannan Fushi to sakin sa ya auku awurin Dukkan Maluma.Fatawa Nurun Alad-darb: 22/126

2. Na Biyu: Fushi da Ke gusar da hankalin mutum; idan Mutum ya saki matarsa a halin Fushi mai tsanani wanda ya gusar masa da hankali, har ya kai ga baisan me yake faɗa ba, wannan saki bai yi ba.

Sheikhul Islam Ibnu Taimiyyah Allah yayi masa rahama yace:

Fushi ya rabu kashi uku: na farko wanda yake gusar da hankali, wanda yayi fushin da baisan me yake faɗa ba, wannan idan yayi saki sakin bata auku ba, babu tsaɓani akan hakaAlmustadrak Ala Majmu’u Fatawa: 5/6

Ibnu Qudama yace:

Maluma sunyi Ijma’i kan cewa wanda hankalinsa ya kau ba ta hanyar kayan maye ba ko wani abu mai kama da haka, sakinsa bata aukuwa.Almugni: 7/378

Na UkuFushi mai tsanani wanda baya gusar da Hankali; Ansamu tsaɓani tsaƙanin Maluma kan wanda ya saki matarsa a hali na fushi mai tsanani, amma hankalinsa yana nan, kuma yasan me yake faɗa.

Magana ta farko: wanda ya saki matarsa yayin fushi mai tsanani amma hankalinsa yana jikinsa to matar ta saku, Wannan dukkan Mazhaba guda huɗunnan Shahararru sunyi Ittifaƙi akan haka.

Sukace domin Shari’a ta hau kansa yayin fushi da kuma rashin fushi, matuƙar hankalin sa yana jikin sa.

kuma idan har akace Sakin wanda yayi fushi bata auku ba da kowa idan yayi wani laifi zaice ai na kasance ina cikin fushi neFathul Bari: 9/389

Magana ta Biyu: Wasu maluman suna ga cewa idan mutum ya saki matarsa yayin fushi mai tsanani to bata saku ba,

Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya yace:

Idan har fushin ya canza masa yanayin sa, amma bai gusar masa da hankali ba sakin bai auku ba, domin fushin ne ya Jawoshi ya sanya shi yayi sakin, yayi sakin alhali bayaso.Almustadrak Ala Majmu’u Fatawa: 5/7

Imam Ibnul Qayyim yace:

Fushi ya rabu kashi uku: na farko shine mai kawar da hankali, mai wannan fushin baisan me yake faɗa ba, wannan idan yayi saki a wannan hali to sakin bai yi ba, na biyu: Fushi wanda mutum yana sanin me yake faɗi, sannan kuma yasan me yake ƙudurce wa, wannan Idan mutum yayi saki a wannan yanayi to sakin ya auku, na uku: fushin yayi masa tsanani ya mamaye shi, amma bai kawar masa da hankalinsa baki ɗaya ba, sai dai zai iya shiga tsaƙaninsa da niyyarsa, ta yadda zaiyi nadamar abinda ya aikata yayin da fushin ya kau, to wannan hali akwai abin dubawa, amma magana kan rashin aukuwar saki a wannan hali yana da ƙarfi.Zadul Ma’ad: 5/195

A Taƙaice:

Idan mutum ya saki matarsa yayin fushi Toh hukuncinsa na nan kamar haka:
1. idan ya zamto fushin ya gusar masa da hankali ta yadda yayi sakin ba tare da ya sani ba, to wannan saki bai auku ba.
2. idan kuma ya saketa yayin fushi mai tsanani amma bai gusar masa da hankali ba to akwai tsaɓani kan aukuwar sakin da rashin aukuwar sa.
3. idan kuma ya saketa yayin fushi ba mai tsanani ba, wannan sakin ya auku, babu tsaɓani tsaƙanin Maluma

Domin neman ƙarin bayani sai a Duba littafan da mukayi nuni zuwa gare su.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top