Tambaya: Tauhidi ya rabu kashi nawa?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Babu wani nassi a fili da yazo da rabe raben Tauhidi, shiyasa aka samu tsaɓani tsaƙanin Maluma wurin Rabe Raben Tauhidi, da kuma Sunan da suka sanya musu, wasu sun raba Tauhidi kashi biyu, wasu Uku, wasu huɗu da sama da haka.
Sannan Wurin sanya musu suna ma an samu tsaɓani tsaƙanin maluma.
Amma rabe rabe da yafi shahara kuma yafi dace wa shine rarrabe Tauhidi zuwa gida uku.
Kuma dalilin wa’innan nau’uka na Tauhidi guda uku shine faɗin Allah maɗaukakin Sarki acikin Suratu Maryam aya ta 65
Ubangijin Sammai da ƙassai, da abinda ke cikin su, ka bauta masa, kayi haƙuri ga bautar Sa, Shin kasan wani wanda yake daidai dashi?
Ubangijin Sammai da ƙassai: shine dalili na Tauhidin Rububiyya, ma’ana shine ya halicci bayi, mai kula dasu, shike Azurta su yake basu lafiya yake sauƙar da ruwan sama da sauran Ayyukan da Allah shi kaɗai yake yi.
Ka bauta masa: Wannan ɓangare yana nuni zuwa ga Tauhidin Uluhiyya, Wanda Ma’anar sa shine bautan Allah shi kaɗai kada a haɗa shi da wani.
Shin kasan wani wanda yake daidai dashi?: Wannan yana nuni akan Sunayen Allah da Sifofin sa, ai babu wani wanda yake kwatankwacin Allah. Allah shi kaɗai yake a Sunayen sa da Sifofin sa.
Allah yace:
Babu wani abu wanda yake kwatankwacin Allah
Suratu Shura: 11
Saboda haka rabe raben tauhidi wanda suka fi shahara sune kamar haka:
1. Tauhidur-Rububiyya: imani da Allah shine mai halitta, mai azurta wa, mamallaki mai jujjuya lamuran bayi
2. Tauhidul Uluhiyya: kaɗaita Allah da bauta, kada a bauta wa wani sai Allah
3. Tauhidul Asma’i Wassifat: Shine Imani da sunayen Allah da sifofin sa wanda suka zo acikin Al-Qur’ani da Hadisi.
Wannan shine rabe raben Tauhidi a taƙaice.
Allah shine mafi sani.