Hukuncin Tahajjud shin Bid’ah ne?

Tambaya: Menene Hukuncin Tahajjud a Ramadana? Inda mutane suke haɗuwa a masallatai domin gudanar da Sallah cikin dare, shin Hakan Bid’ah ne?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Qiyamul Layl Ko Tahajjud duka suna ne na Sallah na nafila da akeyi bayan Sallar Isha’i.

Mustahabbi ne mutum yayi wannan sallah, Musamman acikin watan Ramadana.

Sannan kuma an shar’anta yin Jam’i wurin yin wannan sallah acikin watan Ramadan Kamar yadda aka rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma ayyuka na Sahabbai.

Ana yin Sallar Tarawihi ne ko Tahajjud bayan sallar Isha’i sannan kuma bashi da wasu raka’oi Ƙayyadaddu kamar yadda wasu maluman suka tafi, saboda haka mutum zai iya yin duk yawan Raka’oin da ya ga dama ba tare da iyakancewa ba, saboda wani ya tambayi Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da Sallar dare kamar yadda aka rawaito daga Ibn Umar yace:

Wani mutum ya tambayi Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da sallar dare sai yace “Raka’oi biyu biyu ne, idan mutum yaji tsoron Alfijr zai riske shi sai yayi wutiri da guda ɗaya, sai ya zama masa wutirin sallolin da yayi.

Bukhari: 472. Muslim: 749

Wannan Hadisi yana nuna cewa Sallar dare raka’oi biyu biyu akeyi ana sallama a tsaƙanin su, sannan kuma bashi da wani iyaka, gwargwadon yadda mutum ya samu iko zaiyi.

Qiyaamul Layl ana kiran shi Tarawihi.

Dalillin da yasa ake kiranshi Tarawihi shine hutu da akeyi tsaƙanin Raka’oin.

Haka nan Tahajjud ana Kiran shi Qiyaamul Layl, wasu maluman kuma sukace duk Sallah da aka yi shi bayan bacci to ana kiran shi Tahajjud.

Da haka zamu fahimci cewa Tarawihi, Tahajjud da Qiyamul Layl duka suna nufin Salloli na nafilar dare.

Idan mutum ya sallaci dare baki ɗaya yayi daidai, haka nan idan mutum ya sallaci farkon dare yayi, haka nan idan mutum ya sallaci ƙarshen dare shima yayi kuma shine yafi falala. Haka nan idan mutum ya sallaci farkon dare sannan ya kwanta ya tashi ƙarshen dare shima yayi daidai babu wani abu dake nuni akan haramcin hakan.

Akwai wasu maluman da suke ganin cewa Ayi Tarawihi sannan a tashi ƙarshen dare ayi tahajjudi wannan Bid’ah ce idan har anyi sallah raka’oi fiye da goma sha ɗaya, domin suna ganin cewa baya halatta ayi sallar dare fiye da raka’oi goma sha ɗaya, saboda hadisi da aka rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi baya karawa akan raka’oi goma sha ɗaya, acikin ramadana da watan da ba Ramadana ba, zaiyi sallah raka’oi huɗu, kada kayi tambaya game da kyawunsu, da tsawon su, sannan ya sake yin rakao’i guda hudu, kada kayi tambaya game da kyawun su, da tsawon su, sannan sai yayi sallah raka’a uku.


Sahihul Bukhari: 1147 

Da wannan hadisin ne wasu maluman suke ganin cewa baya halatta ayi sallar dare fiye da raka’oi goma sha ɗaya. Wanda wannan magana ne mai rauni, saboda hadisin da muka kawo a baya da Annabi yace “Sallar dare raka’oi biyu biyu ne

Sannan kuma wannan shine aikin Sahabbai da wa’inda suka zo bayan su, sun kasan ce suna yin sallar dare fiye da raka’oi goma sha ɗaya.

Imamut-Thirmidhi yace:

An samu tsaɓani tsaƙanin Maluma kan abinda ya shafi tsayuwar dare cikin watan Ramadan, wasu Maluman suna ganin cewa ayi raka’oi arba’in da ɗaya tare da wutiri, wannan shine magana ta mutanen Madina, kuma da wannan suke aiki awurin su.

Amma mafi yawan maluma suna aiki ne da abinda aka rawaito daga Umar da Aliyu Allah ya ƙara musu yarda da wasun su daga cikin Sahabban Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Shine raka’oi ashirin.

Wannan shine Maganar At-thauri, da Ibnul Mubarak, da Shafi’i

Sunan Tirmidhi: 3/160

Tunda Mun san hukuncin Tahajjud da kuma tsaɓani dake tsaƙanin Maluma kan adadin raka’oin ta, da maganar da tafi inganci da kuma Ma’anar Tarawihi da Tahajjudi, da Qiyamul layl.

Muka ce dukan su suna nufin sallar dare ne.

To tambaya anan shine menene banbancin mutum yayi sallar a farkon dare sannan ya kwanta ya sake tashi a ƙarshen dare? musamman ma a goman ƙarshe na Ramadan?

Wanda wannan shine abinda aka fi sani da Tahajjud a zamanin mu yanzu.

Akwai hadisi ingatacce da yake nuna Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana raya daren sa a goman ƙarshe

An rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance idan goman ƙarshe ya shiga, yana ƙara hazaƙa, ya raya daren sa, sannan ya tashi iyalansa

Bukhari: 2024. Muslim: 1174

Wannan hadisi yana nuna raya dare da Ibada, musamman Sallolin nafila a goman ƙarshe na Ramadan abu ne mai kyau. Sannan kuma duk yadda mutum yaga dama zaiyi, kodai ya raya daren baki ɗaya, ko kuma ya raya farkon daren ko ƙarshe, ko ya raya farkon daren ya kwanta yayi bacci ya tashi a ƙarshen daren yayi ayyukan sa na Ibada. Duka wannan ya halatta.

Idan mutum ya fahimci dukkan bayanan da mukayi a baya zai gane cewa Tahajjudi da akeyi a cikin Ramadana a ƙarshen dare ba abu bane wanda yake sabo, shima wani ɓangare ne na Tarawihi, kamar yadda yake mutum zaiyi ibada cikin dare ya kwanta ya huta ya tashi yaci gaba da ibadun sa.

An rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:

Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace

Idan ɗaya daga cikin ku gyangyaɗi yazo masa alhali yana Sallah to ya kwanta yayi bacci, har sai baccin ya tafi daga idanunsa, domin ɗaya daga cikin ku idan yayi Sallah yana gyangyaɗi zai iya yiwuwa yaje wurin neman Gafarar Allah sai yaje yana zagin kansa.

Bukhari: 212. Muslim: 786

Abin lura anan shine:

Babu iyaka ga raka’oi na tarawihi da mutum zaiyi abisa magana mafi inganci, sannan kuma dukkan dare ana iya yin Sallah aciki, sannan kuma rabe wa tsaƙanin farkon dare da ƙarshen dare ba mutum yana yinsa ne a matsayin hakan Ibada bane, A’a yana yin hakan ne domin ya huta ya cigaba da ibada, domin kuma ya zama ya raya daren sa baki ɗaya.

Abdullahi Bin Amru Allah ya ƙara masa yarda yace, Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Mafi soyuwar Sallah a wurin Allah Shine Sallar Dawud Alihissalam, mafi soyuwar Azumi a wurin Allah shine Azumin Dawud Alaihis-Salam, ya kasance yana bacci rabin dare na farko, sai ya tashi yayi sallah a ɗayan bisa ukun dare, sannan sai ya koma yayi bacci a ɗayan bisa shidan dare

Bukhari: 1131

Wannan Hadisi yana nuna cewa abinda ake buƙata shine mutum ya bauta wa Allah cikin Nishaɗi, in ya ga dama yayi sallar daren sa a farkon dare, ko yayi bacci ya tashi a ƙarshen dare, ko kuma yayi a farkon dare yayi bacci ya tashi a ƙarshen dare ya cigaba da Sallah.

Duka wannan babu laifi yin hakan.

Saboda Haka yin Tarawihi a farkon dare acikin Ramadana da kuma tashi a ƙarshen dare domin cigaba da wannan sallah abune mai kyau, musamman a goman ƙarshe na Ramadana, kamar yadda hadisin da muka kawo a baya ya nuna.

A taƙaice:

Tarawihi, Tahajjudi, da Qiyamul layl duka Ma’anar su sallar dare. Kuma mutum yana da zaɓi yayi su duk lokacin da ya samu sarari, bayan isha’i ko tsaƙiyar dare ko ƙarshe, amma yin sallar a ƙarshen dare shi yafi falala.

Allah shine Mafi Sani.

Domin sanar damu wani kuskure danna nan

Leave a Reply

Scroll to Top