Hukuncin mutum ya roƙa wa kansa Mutuwa

Tambaya:

Assalamu Alaikum Fatan malam Yana lafiya Allah yasa haka amin Allah yakara wa malam fahimta da basira.

TAMBAYATA

Menene halarcin rokawa kanka mutuwa ko rashin tsowon kwana. Nagode

Amsa:

Baya Halatta Mutum ya roƙi Allah ya ɗauki ransa saboda wata cuta ko musiba da ta auka masa. amma idan ya zamto Fitintinun Zamani sukayi yawa, mutum yana tsoron Rasa Addinin sa to a wannan yanayi babu laifi, ko kuma saboda shauƙin haɗuwa da Allah, ko kuma begen yin shahada.

Babu wata rai da zata mutu sai idan kwanakin da Allah ya yanke mata ya cika. Kamar yadda Allah yayi bayani acikin ayoyi na AlQur’ani Masu yawa, Haka nan Hadisan Annabi Sunzo da tabbatar da Haka.

Allah yace:

Kowace Al’umma tana da Ajali, idan Ajalinsu yazo baza’a yi musu jinkiri koda na ɗan lokaci kaɗan ne, sannan kuma ba zasu gabaci ajalin su ba

Suratul Araf: Aya 34

Saboda haka kowani abu na da Ajalin da Allah ya sanya masa. Ba zai riga wannan Ajalin ba, sannan baya jinkiri.

An rawaito hadisai masu yawa kan haramcin mutum ya roƙa wa kansa mutuwa, daga cikin wannan Hadisai:

Anas Bin Malik ya rawaito daga Annabi tsira da Amimcin Allah su tabbata a gare shi yace:

Kada ɗaya daga cikin ku yayi begen ya mutu saboda wani cuta da ta sauƙa masa, idan ya zama babu yadda zaiyi sai yayi begen ya mutum to yace: “Ya Allah ka rayar dani matuƙar rayuwa itace tafi alheri a gareni, ka kashe ni matuƙar mutuwa itace tafi alheri a gare ni.

Sahihul Bukhari: 6351. Sahih Muslim: 2680

Wannan Hadisi ya nuna cewa baya Halatta mutum ya roƙi Allah ya ɗauki ransa saboda wata musiba ko ciwo da ya shafe shi, sai dai yayi Addu’a ya nemi zaɓin Allah.

Amma idan mutum yana begen mutuwa ne saboda fitintinu sunyi yawa, Yana tsoro kada Ya rasa Imanin sa to wannan Babu laifi mutum ya nemi Allah ya ɗauke shi kafin Fitinar ta riske shi.

Kamar Yadda Abdullahi Bin Abbas ya Rawaito daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, Allah ya umar ce shi yace:

Idan kayi nufin Fitina ga bayin ka to ɗauke ni zuwa gare ka ba tare da an fitine ni ba

Attirmidhi: 3233. Ahmad: 3484

Haka nan idan mutum yana begen Mutuwa ne saboda ya samu shahada to shima babu laifi, kamar a fita Jihadi mutum ya roƙi Allah ya sanya shi cikin shahidai.

Haka nan Neman mutuwa saboda shauƙin Haɗuwa da Allah, shima wannan Babu laifi.

Kamar yadda yake acikin Hadisin Ammar bin Yasir ya rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a garwshi. Yake cewa aciki:

Ina roƙon ka shauƙin haɗuwa da kai

Annasa’i: 1305. Ahmad: 18351

Kuma an rawaito athar masu yawa daga magabata wanda yake nuna shauƙin su na haɗuwa da Allah. wanda kuma ba’a haɗuwa da Allah har sai an Mutu.

Kuma ƙin Mutuwa da Tsoron haɗuwa da Allah yana daga cikin abinda Allah ya zargi yahudawa dashi kamar yadda yayi bayani acikin suratul Baqara aya ta: 94.

Amma idan mutum yana begen mutuwar ne ba domin wata cuta ko musiba ba, haka nan ba domin abubuwa da muka ambata a sama ba to akwai tsaɓani a tsaƙanin maluma kan halaccin sa da rashin halaccin sa.

A taƙaice:

Baya halatta mutum yayi begen mutuwa ko ya roƙi Allah ya kashe shi saboda wata cuta ko Musiba da ta auka masa, amma ya Halatta Mutum yayi begen Mutuwa domin neman Shahada, ko domin son haɗuwa da Allah, ko domin gudun fitina.

Sannan Ka sani cewa tsawon kwana ga Mumini Alheri ne, domin hakan zai bashi daman ayyuka na alheri masu yawa.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top