Hukuncin Auren Mutu’a

Tambaya: Menene Auren Mutu’a kuma meye hukuncin sa?

Amsa: Auren Mutu’a shine na miji ya auri mace zuwa wani loci ƙayyadadde, abisa wani dukiya da zai bata.

Hukuncin Auren Mutu’a a Shari’ar Musulunci:

Auren Mutu’a halal ne a farkon Addinin Musulunci, amma daga baya aka shafe Hukuncin sa. Kuma Allah ya halatta ne saboda buƙatuwar sa a wannam lokaci da aka halatta. daga baya kuma aka haramta.

An rawaito daga Aliyu Bin Abi ɗalib Allah ya ƙara masa yarda yace:

Lallai Annabi ya Hana auren Mutu’a, da Kuma cin naman jakin gida, a lokacin Khaibar.

Sahihul Bukhari: 4216

Sannan an sake rawaito wa daga Sabura bin Ma’abad yace mahaifin sa ya bashi labari cewa Annabi Yace:

Yaku Mutane, lallai ni na kasan ce na muku Izini kan Mutu’a, to lallai Allah ya haramta haka har zuwa ranar tashin Alqiyama, duk wanda ya kasance akwai wasu mata a tare dashi ta hanyar mutu’a to ya rabu dasu, sannan kada ku ɗauki wani abu daga cikin abinda kuka basu

Sahihu Muslim: 1406

Wa’innan Hadisai suna tabbatar da Haramcin Auren Mutu’a har zuwa ranar tashin Alƙiyama.

Sannan kuma auren mutu’a yana da illoli masu yawan gaske, wurin tauye haƙƙoƙin mata, da kuma yaran da za’a haifa ta yadda mutum zai iya tara wa da macen da ya ga dama a kowani lokaci, kuma ya tafi ya barta ba tare da kula da ita ba.

Saboda Haka kada Mutum ya ruɗu da shubuhohin da ƴan Shi’a suke kawo wa domin halatta wannan Aure. Haramun ne.

A taƙaice:

Auren Mutu’a an Halatta shi a Farkon Musulunci, amma daga baya aka haramta, saboda haka auren Mutu’a Haramun ne har zuwa ranar tashin Alƙiyama.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top