Wajibi ne yiwa iyaye biyayya cikin abinda bai tsaba wa Allah ba

Tambaya

Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuh Barka da warhaka.
Sunana……….. daga Zamfara state.

Tambayata itace
Malan mahaifinane yana daukan abubuwanda matane ke fada akanmu ni yan uwana har ta gaharamta mana yin sallah a masallacin ahlussunnah saboda a inda muke rayuwa yan gargajiya sunfi yawa

Ena karantawa awani masallaci bayan magrib amma sunsa yahanani

Sunsa yayiman magana akan idan naqara sallah wajen yan izala baiyafemanba

Malam ya zanyi kuma wallahi mutane ne suke sashi yakeman komai domin ada babu ruwanshi da abinda nakeyi amma dasuka sanigaba saida nadaina karantarwar yanzun haka

Amsa

Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Allah maɗaukakin sarki ya wajabta wa ɗa yin biyayya ga iyayen sa, da kuma kyautata musu acikin ayoyi masu yawa acikin Alqur’ani mai girma, haka nan Hadisan Annabi tsira da Amincin Allah su Tabbata a gare shi sunzo da umarnin yiwa iyaye biyayya.

Allah yace:

Ku bauta wa Allah kada ku haɗa shi da kowa, sannan iyaye su biyu ku kyautata musu

Suratun-Nisa: 36

Saboda haka tsaɓa wa mahaifa yana daga cikin manyan laifuka da zai shigar da mutum wuta.

Amma sai dai Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam yace:

Ana yin ɗa’a ne cikin Abinda Bai tsaɓa wa Allah ba.

Sahihul Bukhari: 7257

Saboda Haka ba’a yin ɗa’a wa wani wurin tsaɓa wa Allah.

yin biyayya ga iyaye yana iyaka, da zarar zai kai ga tsaɓa wa Allah to baya halatta ayi musu ɗa’a.

Allah Maɗaukakin sarki yace:

Munyi wasiyya(Umarni) ga Mutum ya kyautata wa iyayen sa, Amma idan suka tsananta maka kan cewa ka haɗa ni da wani wurin bauta to kada kayi musu ɗa’a

Suratul-Ankabut: 8

Iyaye ana kyautata musu, amma idan suka umarci mutum da saɓon Allah to bazai yi musu ɗa’a ba, amma kuma duk da haka bazai yi musu wani abinda zai muzguna musu ba, zaiyi iya ƙoƙarin sa wurin fahimtar dasu gaskiya, da kuma roƙon Allah ya shiryar dasu.

Saboda Haka umartan ka da mahaifin ka yayi na cewa kada ka rinƙa zuwa Masallaci na Ahlussunnah kayi Sallah wannan bai dace ba, ya kamata ka zauna dashi ka bashi haƙuri ka nuna masa Muhimmancin barin ka kaje kayi Sallah a masallacin da ya kwanta maka a rai, domin hakan zai fi samar maka natsuwa acikin zuciyar ka yayin Sallar. Idan yaƙi to babu laifi kaci gaba da zuwa Masallacin ka, sai dai kuma sai ka rinƙa kauce wa idanun sa saboda kada hakan ya ƙara zafafa rashin fahimtar juna dake tsaƙanin ku. Sai kayi ta ƙoƙari wurin fahimtar dashi da kuma roƙon Allah ya sanyaya zuciyar sa.

Haka nan karantar wa da kake yi, shima ka zauna dashi ka fahimtar dashi muhimmancin ya barka kaci gaba da karantarwarka.

Sannan kuma idan kasan masu zuga shi sai ka samesu kayi musu nasiha kan Hatsarin abinda sukeyi na Annamiman ci, wanda yana daga cikin Manyan laifuka.

Abu mai mahimmanci kamar yadda nayi bayani a sama shine ka rinƙa samun mahaifinka kuna tattauna wa, sannan kana ƙoƙarin kwantar masa da hankali, sannan kuma ka yawaita roƙon Allah ya daidaita tsaƙanin ku. Insha Allah, Allah zai kawo maka Mafita.

A taƙaice

Anayin ɗa’a ne wa iyaye kan abinda bai tsaɓa wa Allah ba, amma idan suka umarci mutum da abinda ya tsaɓa wa Allah to bazai yi musu ɗa’a ba. Amma kuma ba zai muzguna musu ba.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top