Hukuncin yin sallar tarawihi raka’oi hudu a jere

Tambaya: menene hukuncin yin sallar Tarawihi raka’oi huɗu a jere?

Amsa: da sunan Allah mai Rahama mai Jin Kai.

an rawaito wani Mutum ya tambayi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi game da sallar dare yaya akeyi sai Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:

Sallar dare Raka’oi biyu biyu ne.

Sahihul Bukhari: 472 

wannan hadisi yana nuna cewa Sunnah a sallar dare shine a yi shi raka’oi biyu biyu sannan sai ayi wutiri da guda daya a karshe.

amma an rawaito hadisi daga Aisha Allah ya kara mata yarda an tambaye ta yaya sallar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yake acikin watan Ramadana? sai ta amsa tace:

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi baya karawa akan raka’oi goma sha ɗaya, acikin ramadana da watan da ba Ramadana ba, zaiyi sallah raka’oi huɗu, kada kayi tambaya game da kyawunsu, da tsawon su, sannan ya sake yin rakao’i guda hudu, kada kayi tambaya game da kyawun su, da tsawon su, sannan sai yayi sallah raka’a uku.

Sahihul Bukhari: 1147 

a karkashin wannan Hadisi ne wasu maluman suke ganin cewa mutum zai iya yin sallar tarawihi rakao’i guda huɗu a jere babu sallama a tsakanin su.

amma a hakikanin lamari wannan hadisi baya nuna haka, yana nuna cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana yin rakao’i biyu ne sai yayi sallama sannan ya kara yin wasu biyu sai yayi sallama sannan sai ya huta bayan raka’oi huɗun, kafin ya tashi yaci gaba. kamar yadda mukayi bayani a hadisin da ya gabata cewa Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace sallar dare raka’oi biyu biyu ne.

Ibnu Baɗɗal Allah yayi masa rahama yace:

Faɗin Aisha Allah ya ƙara mata yarda ” Yana sallah raka’oi hudu” ana ɗaura shi akan faɗin Manzon Allah ” Sallar dare raka’oi biyu biyu ne ” domin shi wannan yana fassara wannan hadisin farkon ne, wanda yake yazo a dunƙule.

sannan kuma bayanin wannan yazo a wasu bangarori da hanyoyin da aka rawaito hadisin, kamar hadisin da aka rawaito daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace ” Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana yin sallah rakao’i goma sha daya da dare, tare da wutiri. yana yin sallama tsakanin rakao’i guda biyu

Sharh Sahih Muslim: 3/142

Al’adawy yace:

Zai yi sallama bayan kowani raka’a biyu, sannan an ƙi mutum ya jinkirta Sallama zuwa bayan raka’oi huɗu

Hashiyatul Adawy: 3/442

An tambayi Sheikh Ibn Baz Allah yayi masa rahama game da limaman da suke haɗa rakao’i huɗu ko fiye da haka kafin suyi Sallama, kuma suna riya cewa hakan yana daga cikin Sunnah, menene hukuncin hakan?

Ya amsa (a taƙaice)

Wannan ba’a shar’anta shi ba, makruhi ne ko kuma ma haramun ne a aikata hakan, awurin da yawa daga cikin maluma, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace “Sallar dare raka’oi biyu biyu ne”.

Sannan kuma saboda hadisin da aka rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:

“Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana sallah raka’oi sha ɗaya da dare, yana yin sallama bayan raka’oi biyu sannan sai yayi wutiri”

Amma hadisin da aka rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace “Annabi ya kasance yana yin sallar dare raka’oi huɗu kada ka tambaya game da kyawun su da tsawon su, sannan ya sake yin Salloli raka’oi huɗu kada ka tambaya game da kyawun su da tsawon su” abinda take nufi da wanna hadisi shine

Yana sallama ne bayan kowani raka’a biyu, ba yana nufin cewa yana yin raka’oi huɗu ne a jere da Sallama ɗaya ba saboda hadisin da ya gabata, da kuma Hadisin da Annabi yace “ Sallar dare raka’oi biyu biyu ne

Fatawa Ibnu Baz: 30/38

A taƙaice:

Sallar Tarawihi da Sallar dare baki ɗaya anayin su raka’oi biyu biyu ne sai ayi wutiri a ƙarshe. Ba’a haɗa rakao’i huɗu ko fiye da haka a jere kafin ayi sallama. Wannan shine magana mafi inganci.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top