Yadda ake wankan janaba

Siffar wankan janaba ya rabu kashi biyu:

Na farkowanka wanda yake wadatarwa; duk wanda yayi wannan wankan to ya wadatar dashi. Shine Mutum ya ƙudurce Niyyar wankan Janaba, sai ya wanke jikinsa baki ɗaya. Ko ya tsaya a ƙarƙashin shower ya wanke jikin sa. Wannan ya wadatar dashi. Idan Mutum yayi haka to ya tsarƙaƙa. Wasu Maluman kuma sunaga sai ya Kurkure bakin sa ya shaƙi ruwa a hancin sa.

Na biyu: Wanka Cikakke; Shine wanda ya ƙunshi Wajibai Mustahabbai

Yadda ake yin wanka cikakke

Mutum zai wanke hannu kafin ya shigar dashi Kwanon wanka, sannan ya ɗebi ruwa ya zuba a farjin sa ya wanke sau uku, sannan sai yayi alwala irin alwalar Sallah cikakke, ko ya jinkirta wanke ƙafa zuwa ƙarshen wanka, ko ya wanke a lokacin. Sannan ya ƙwarara ruwa sau uku a kansa ya tsefe suman kan shi har sai ruwan ya game kanshi, sannan ya zuba ruwa a gefenshi na dama, sannan ya zuba a gefen hagu. 

Wannan shine wanka cikakke. An rawaito wannan irin wanka daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi. a duba Sahihul Bukhari: 317.

Amma wanda ya taƙaita akan wanka na farko to ya wadatar.

Allah shine Mafi Sani. Idan akwai wani Kuskure zaku iya danna nan domin tuntuɓar mu.

Leave a Reply

Scroll to Top