Hukuncin Niyya a sallar ƙasaru

Tambaya: Shin dole sai anyi niyya wa sallar ƙasaru? kuma yaya akeyi idan ana yi?

Amsa: Da Sunan Allah mai Rahama mai jin Kai.

An samu tsabani tsakanin Maluma kan hukuncin wajabcin yin niyya domin sallar ƙasaru.

Magana ta farko: Sukace yin niyyan sallar ƙasaru yayin ƙabbarar Harama sharaɗi ne na ingancin Sallar, saboda Asali a Sallah shine cikawa, idan mutum bai ƙudurce Niyyar ƙasaru ba yayin ƙulla Sallah to Sallar sa zai ƙullu ne kan yin Sallah cikakke. Saboda Haka dole wanda zai ƙasaru sai ya ƙudurce Niyyar Ƙasaru yayin Yin ƙabbarar Haraman sa.

Imamun-Nawawi yace:

Mazhabin mu shine baya halatta mutum yayi ƙasaru har sai ya ƙudurce niyyar ƙasaru yayin fara sallar sa. Al-Abdary yace: haka da yawa daga cikin Maluman Fiqhu suka faɗa

Al-Majmu’: 4/353

Yaya Akeyin Niyyar Ƙasaru?

Niyyar ƙasaru kamam niyyar sallar yake, ba sai mutum ya furta ba, da zarar Mutum yazo sallar zai ƙudurce acikin zuciyarsa cewa wannan Sallar zai Sallace ta ƙasaru. Shikenan.

Magana ta biyu: sukace Sallar ƙasaru bata buƙatar wata Niyya saboda dalilai kaman haka:

  • Na ɗaya: Domin Ƙasaru yayin tafiya shine asali a Sallah, saboda haka baya buƙatar wata Niyya.
  • Na biyu: Kamar yadda mazaunin gida ba sai yayi niyyar cika sallah ba, haka nan matafiyi ba dole sai yayi niyyar yin ƙasaru ba
  • Na Uku: Ba’a rawaito Annabi yana Umartar Sahabban sa idan zasu yi ƙasaru cewa sai sunyi wata Niyya ba, haka nan ba’a rawaito daga Khalifofin sa ko Tabi’ai cewa suna umarni da haka ba.

Wannan itace fatawa ta Mazhabar Hanafiyya, da wata Riwaya da Aka rawaito daga Imam Ahmad, kuma wannan Fatawar Sheikhul Islam ya zaɓa, da Sheikh Ibnu Uthaymeen

Al-insaf na Mardawy: 2/228. Majmu’u Fatawa: 24/16. Sharhul Mumti’ Ibn Uthaymeen: 4/371

A taƙaice

Niyyar Sallar ƙasaru kaman Niyyar Sallar ne, mutum zai ƙudurce a Zuciyarsa cewa zai yi Wannan Sallar ne Ƙasaru.

Allah shine mafi sani

Leave a Reply

Scroll to Top