Shin Taba mace yana karya Alwala?

Tambaya: Asslm
Barka da wan nan lokacin fatan mal ya wuni lfy allah yasa ameen
Allah yakarawa karatu albarka
Tambayata itace dan. Allah shin idan mutum yana da al.wala sai yayi wasa da matarsa. Amman batare da maziyi ko wadiyi ko maniyi yafitaba . Amman kuma yaji dadi ajikinsa . ya matsayin al.walarsa take

Amsa: Maluma sun samu tsaɓani kan shin taɓa mace yana warware alwala? Akwai maganganu guda uku:

Amma magana mafi inganci game da Wannan Hukunci sune kamar Haka:

Na Farko: Idan Mutum ya shafi mace da Sha’awa to Alwalar sa ta karye, Amma idan ba da Sha’awa ya shafi mace ba to alwalar sa bata karye ba.

Wannan shine zai bada dama wurin haɗa nassoshi da suka zo kan wannan Mas’ala.

Faɗin Allah acikin Suratun-Nisa

Ko kuwa kun shafi mata

Suratun-Nisa: 43

Wannan Ayah tana Nufin Jima’i ne ba shafa kawai ba. Kamar yadda Ibnu Abbas ya fassara.

Na Biyu: Shafan mace baya karya alwala, ko mutum ya shafi macen da sha’awa ne ko ba da Sha’awa ba.

Sun kafa Hujja kan cewa Asali shine Tabbatuwar tsarƙi ga wanda yake da tsarƙi har sai an samu dalili da yake nuna warwarewar tsarƙin. Kuma anan babu wani Hujja da yake nuna shafan mace yana warware Alwala.

Sannan An rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:

Na kasance ina bacci a gaban Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Ƙafafu wa na suna Ƙiblar sa, idan yazo yin Sujada sai ya ɗan tukuɗe ni da yatsun sa sai na ɗage ƙafafu na, idan ya tashi sai na shimfiɗa ƙafafu na.

Sahihul Bukhari: 382

Wannan Hadisi yana nuna cewa Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya taɓa ta alhali yana Sallah. Kuma da taɓa mace yana warware alwala da alwalar sa da Sallar sa ya ɓaci.

Haka nan akwai Hadisi da aka sake rawaito wa daga ita Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:

Wata rana na duba Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam akan shimfiɗar kwanciya sai bangan shi ba, sai na fara laluɓe ko zan ji shi, sai hannuna ya faɗa kan ƙafar sa, yana Sujjada.

Sahih Muslim: 486

Wannan Hadisi yana sake nuna cewa Aisha Allah ya ƙara mata yarda ta taɓa Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana Sallah, kuma bai yanke Sallar ba ya sake alwala, wannan yake nuna cewa alwalar sa bata karye ba domin da zai yanke Sallar yaje yayi alwala, amma baiyi hakan ba.

Sannan An sake rawaito wa daga A’isha Allah ya ƙara mata yarda tace:

Lallai Annabi ya sumbaci wata daga cikin matayen sa, sannan ya fita yaje Sallah, bai sake alwala ba.

Abu dawud: 179

Wa’innan hadisai duk suna nuna cewa Taɓa mace baya karya alwala.

Saboda haka a taƙaice Amsar Tambayar ka: idan mukayi amfani da magana ta farko alwalar ka ta ɓaci, domin kunyi wasa, kuma kaji daɗi. Amma a magana ta biyu kuma alwalar ka tana nan domin maziyyi ko maniyyi bai fita maka ba.

Allah shine mafi sani

Leave a Reply

Scroll to Top