Tambaya: Menene Hukuncin kame baki Ranar Sallar layya har sai an sauƙo daga Sallah?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Sunnah ce a kame baki ranar sallar layya har sai an sauƙo daga Sallah. Haka nan idan Mutum zai yi layya Sunnah ce a gare shi ya kame bakin sa, sannan ya buɗe bakinsa da naman layyan sa.
An rawaito daga Buraida Allah ya ƙara masa yarda yace:
Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance baya fita zuwa Masallaci ranar idin Azumi har sai yaci abinci, baya cin abinci ranar idin layya har sai yayi Sallah.
Tirmidhi: 542
Wannan Hadisi ya nuna cewa Sunnah ce kame baki a Sallar Layya.
Yazo acikin Mausu’atul Fiqhiyya sukace:
Wanda yake da abinda zai yanka na layya to Maluman fiqhu sunyi ittifaƙi kan cewa Sunnah ce a gare shi ya jinkirta cin abinci ranar Sallar layya ya kame ga cin abinci domin ya buɗe bakin sa da Hantan Abinda ya yanka saboda Hadisin da Aka rawaito daga Buraida.
Mausu’atl Fiqhiyya: 341
Allah shine mafi sani.