Fuskantar Alqibla yayin Yanka dabba

Tambaya: Menene Hukuncin Fuskantar Alqibla yayin yanka?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Sunnah ce yayin yanka a juyar da dabbar da za’a yanka ta fuskanci Alqibla, amma ba wajibi bane, idan Mutum ya yanka dabbar sa ta kowace jiha yankar sa tayi, amma ya bar Sunnah.

Yazo acikin Al-Mausu’atul Fiqhiyya. Suka ce:

Yana daga cikin ladubban yanka; mai yankan ya fuskanci Alqibla, haka nan abinda za’a yankan ta zamo tana fuskantar Alqibla ta wurin yankan, ba fuskan ta ba. Domin Alqibla jiha ce da ake kwaɗayi zuwa ga yi wa Allah ɗa’a. Sannan kuma Ibnu Umar Allah ya ƙara masa yarda ya kasance yana ƙin cin abinda aka yanka ba’a fuskanci Alqibla ba, kuma ba’a samu wanda ya tsaɓa masa ba daga cikin Sahabbai, haka nan hakan ya inganta daga Ibnu Sirin, da Jabir bin Zaid. A duba Mugni: 3/221

Mausu’atul Fiqhiyya: 21/196

Hakanan yazo a fatawar Lajnatud-da’imah akayi musu Tambaya game da Mutumin da yayi yanka bai fuskanci Alqibla ba, suka bada fatawar cewa yankan sa tayi, sai dai ta tsaɓa wa Sunnar Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi. A duba Fatawa Lajnatud-da’imah: 22/477

A taƙaice

Sunnah ce idan Mutum zai yanka dabba ya fuskantar da Wuyan dabbar ta Alqibla. Amma idan mutum yayi yanka ta wata jiha ta daban, yankan sa tayi, amma ya tsaɓa wa Sunnah.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top