Hukuncin Cin Abincin Kirismeti da Taya masu yi Murna

Tambaya: shin ya Halatta cin yanka da akayi domin Kirismeti ko kuma a taya wa’inda suke yi Murna?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Da farko Allah maɗaukakin sarki ya Halatta wa Musulmai cin yankan Ahlul kitabi matuƙar basu ambaci sunan wanin Allah ba yayin yankan.

Allah maɗaukakin Sarki yace:

A yau an Halatta muku Abubuwa tsarƙaƙa masu dadi, kuma abincin wa’inda aka baiwa Littafi halal ne a gare ku.Suratul Ma’ida Ayah ta 5

Da wannan Ayah ne Maluma suka kafa hujja kan halaccin cin yankan Yahudu da Nasara matuƙar dai basu ambaci sunan wanin Allah yayin yankanba, ko kuma basuyi yankan domin wanin Allah ba.

Domin Allah ya hana cin duk wani yanka da aka ambaci sunan wanin sa akai.

Allah maɗaukakin Sarki yace:

Kada kuci daga abinda ba’a ambaci sunan Allah a kansa ba, lalle hakan Fasikanci neSuratul An’an 121

Saboda haka idan akayi yanka aka ambaci sunan wanin Allah akai to Haramun ne Musulmi yaci wannan yanka. Koda ko Musulmi ne ya yanka.

Abisa bayanan da mukayi a sama zamu fahimci cewa Cin yankan Ahlul kitabi halal ne.

Sai dai Tambaya itace Ya Halatta aci yankan da sukayi domin kirismeti ko wasu bukukuwan su?

Bai halatta ba, domin wannan yanka ne da sukayi domin tsaɓa wa Allah, kuma sunyi yankan ne don wanin Allah, saboda haka baya halatta aci wannan yanka.

An Tambayi Maluma Masu Fatwa ta Lajnatud-da’imah kan Halaccin cin abincin da aka yi shi domin haramtattun bukukuwa sai suka ce.

Baya Halatta ga Musulmi yayi duk wani abu da zai ɗaukaka alamomi na kafurci ko shirka, yana daga Cikin haka wasu harkoki na Addini kaman Bukukuwar Idi na kafirai da makamantar sa.

Haka nan duk wani abinda aka tanada domin bukukuwa na Shirka ko na Bid’ah baya halatta aci domin hakan yana nuna goyon baya da yarda da abinda wa’innan Kafirai suke kai.

Abinda ya zama wajibi ga Musulmi shine ya kiyaye ya zama mai tsantseni game da Addinin sa,Fatawa Lajnatud-da’imah: 1/450-451

Imam Ibnu Taimiyya Allah yayi masa Rahama yayi bayani acikin Littafinsa Iqtida’u siradil Mustaqeem kan wannan magana: gashi a taƙaice.

Abinda ya halatta aci na kyautar da Ahlul kitabi zasu bayar ranar Idin su shine abubuwa wanda ba’a yanka ba, kaman abinda zasu saya su bada kyautar sa, amma abinda suka yanka domin idin su ko kuma domin neman kusanci zuwa ga wanin Allah to ansamo riwaya Biyu daga Imam Ahmad, wanda yafi shahara shine Wanda yake nuni kan Haramcin cin sa, koda ko ba’a ambaci sunan wanin Allah akan sa ba, haka nan an naƙalto hani ga cin wannan yanka daga Aisha da Ibnu Umar Allah ya ƙara musu yarda.Iqtida’u Tsiradil Mustaqeem: 1/251

Duka wannan fatawoyi sunan nuna Haramcin cin yankan da akayi ranar kirismeti.

Amma idan ba ranar kirismeti bane babu laifi.

Amma game da taya su murnan wannan rana, shima Haramun ne, domin abinda suke yi tsaɓon Allah ne mai girma shine danganta wa Allah ɗa, wanda hakan kafirci ne da Kuma zagin Allah, saboda haka baya halatta a tayasu murna kan wannan Mummunan aiki da sukeyi.

Kamar mutum ne ko wani shekara in ta kewayo ya kan haɗa biki ya tara mata yayi ta zina dasu, kai kuma sai kazo kana tayashi murnan zagayowar wannan rana, da taya shi farin ciki kan abinda yake aikata wa, wanna Baya Halatta.

A taƙaice:

Cin yankan Ahlul kitabi ya Halatta idan har basu ambaci sunan Wanin Allah akan yankan ba, amma yanka da sukeyi ranar Bukukuwar su baya halatta aci, domin bukukuwa ne na tsaɓon Allah, kuma yanka ne da akayi domin wanin Allah,
Haka nan Baya halatta a taya su murna kan wannan bukukuwa tasu, domin hakan tayasu ɓarna ne, da kuma ƙara ƙarfafa musu guiwa.

Allah shine Mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top