Watan rajab: Falalar sa da kuma bid’oi da akeyi acikinsa da Hukuncin Azumin Tsaffi

Watan rajab yana daga cikin watanni masu Al-farma guda huɗu a musulunci, wanda Allah ya karrama su akan sauran watanni. Wa’innan watanni masu alfarma sune kamar haka:

  • Dhul Qa’adah
  • Dhul Hijja
  • Al-Muharram
  • Rajab

Wa’innan watanni haramun ne ga Musulmai su fara kai farmaki a cikinsu, kuma aikin alheri acikin wa’innan watanni suna da falala matuƙa, haka nan aikata laifi acikinsu na da Girma.

Shin watan rajab na da wata falala ta daban bayan wa’inda muka ambata?

Haƙiƙa akwai da yawa daga cikin mutane wa’inda suke riya cewa Watan rajab na da wata falala ta daban wanda babu a sauran watanni, sukan ƙebance wannan wata da wasu nau’uka na ibada, kaman Azumi, Salloli da dai sauransu. To haƙiƙa babu wani abu da ya inganta na keɓance wannan wata da irin wannan ibada. Duk hadisan da sukazo akan haka masu rauni ne ko na Karya kamar yadda maluma sukayi bayani.

Imam Hafiz ibn Hajar yace:

Babu wani hadisi da za’a iya yin hujja dashi da yazo game da Keɓance watan rajab da wani azumi, ko zikiri, ko sallar dare, kuma Imam Abu Isma’il Al-Harawi ya rigani tabbatar da wannan maganaA duba littafin: Tabyinul ajab bima warada fi shahri rajab Shafi na 23

Wasu ayyuka da akeyi na Bid’ah acikin wannan wata:

  • Salatu-rraga’ib: Wannan wata sallah ce wanda aka ƙirƙiro ta, wacce bata da asali daga Al-ƙur’ani ko Sunnah. Sheikhul Islam ibn taimiyya Allah ya rahamshe shi yace:

Amma wannan sallah da ake kira salatu-rraga’ib bata da asali, fararriyar aba ce, bata halatta ayi ta.Majmu’ul fatawa: 23/132

  • Keɓance wannan wata da wani Azumi ko itikafi: Kamar yadda mukayi bayani a baya cewa babu wani hadisi ingatacce da yayi nuni da keɓance wannan wata da wani azumi, kamar azumin tsaffi da sauransu, haka nan babu wani hadisi ingatacce da yayi nuni da yin itikafi acikin wannan wata. Sai dai yin azumi acikin watan kaman ko wani wata ba tare da ƙebanceshi ko riya cewa yana da wani falala ta daban fiye da sauran watanni masu alfarma ba abu ne mai kyau.
  • Yin bikin ranar Isra’i da Mi’iraji: biki don tuna rananr da akayi isra’i da Mi’iraji da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama shima bai tabbata an rawaito Annabi ko Sahabbai sunayi ba a wannan wata. Saboda haka bid’ah ce da ya kamata Musulmi ya kaurace mata.

A taƙaice:

Watan rajab wata ne mai Alfarma kuma ana son musulmi ya yawaita ibada aciki, sannan ya kauce wa saɓon Allah, haka nan yana da kyau musulmi ya ƙaurace wa duk wata bid’ah da ake aikatawa cikin wannan wata, ya tsaya kan Sunnah. Yana da kyau a yawaita azumi da nafiloli da ayyuka na alheri kamar sauran watanni masu alfarma ba tare da keɓance shi watan rajab ɗin shi kaɗai ba.

Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Scroll to Top