Hukuncin fitsari a tsaye

Mai Tambaya: Ya Halatta Mutum yayi fitsari a tsaye?

Amsa: Babu laifi mutum yayi fitsari a tsaye musamman ma idan akwai buƙatar hakan, Misali yana wurin da tsugunawa zatayi masa wuya ko akwai wata lalura, amma da sharaɗi ya zamto ya suturce al’aurar sa, kada wani ya gani. Sannan kuma fitsarin bazai fantsamu zuwa jikin sa ba.

An rawaito daga Huthaifa Bin Yaman Allah ya ƙara masa yarda yace:

Na kasance tare da Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi sai yaje wurin zubar da sharan wasu Mutane sai yayi fitsari a tsaye

Sahihul Bukhari: 224,. Sahihu Muslim: 273

Wannan Hadisi ya nuna ƙara cewa Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yayi fitsari a tsaye saboda buƙatar hakan tsaɓanin Yanda ya saba yi a tsugune. Domin Sunnar Annabi shine yin fitsari a tsugune sai dai idan akwai lalura.

Saboda haka yin fitsari a tsugune shine yafi domin shine galibin yanayin da Annabi yake fitsarin sa, kuma hakan yafi suturce al’aurar mutum kuma yafi kiyaye shi daga watsuwar fitsari a jikin sa.

Leave a Reply

Scroll to Top