Habbatus-Sauda Waraka ce ga dukkan Cututtuka

Tambaya: Shin Habbatus-Sauda tana maganin ko wani irin ciwo?

Amsa: An rawaito Hadisi daga Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam kan falalar Habbatus-Sauda.

An rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:

Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Habbatus-sauda Waraka ne na kowani ciwo sai dai mutuwa

Sahihul Bukhari: 5687

Wannan hadisi yana nuna falalar Habbatus-sauda kuma tana maganin cututtuka da yawa.

Ibnul Qayyim Allah yayi masa Rahama yace:

Faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama “Waraka ce ga kowani cuta” misalin sa shine Faɗin Allah acikin Suratul Ahqaf: Aya ta 25

Tana Dirkake dukkan wani abu da umarnin Ubangijin ta

Ma’ana duk wani abu da Allah ya ƙaddara zata dirkake amma ba komi ba.

Duba zadul ma’ad: 4/297

Wannan yana nufin ita Habbatus-sauda magani ce ga dukkan ciwo da Allah ya ƙaddara zata warkar.

Ya rage kuma ayi bincike ta yaya za’a yi amfani da ita wurin yin maganin.

Sannan Kuma kamar yadda abu ne sananne akan samu magani yana aiki amma kuma ba ga kowa yake yi ba, wani zaiyi amfani da shi ya warke wani kuma yayi amfani dashi amma ba zata yi masa tasiri ba.

Sheikh Bin Baz yace:

Da yawa daga cikin mutane sabbuba basu amfanar su, hakanan Ruƙiyya da akeyi da Alqur’ani bata yi musu amfani ko kuma wanin sa, domin rashin samun sharaɗi, inda ace kowani mara lafiya yana warke wa da Ruƙiyya ko magani da babu wanda zai mutu da ciwo, amma Allah maɗaukakin sarki a hannun sa waraka yake, idan yayi nufin mutum ya warke sai ya sauƙaƙe masa sabbuban sa, amma idan baiyi nufin haka ba to wannan sabbuba na warakar ba zata amfanar da mutum ba

Majmu’u fatawa Bin Baz: 8/61

Wannan yana nuna cewa ba kowa bane Addu’a ko magani yake yi masa amfani. Wani zaisha tayi masa amfani, wani kuma zai sha bazata yi masa amfani ba saboda rashin samun sharaɗin yin aikin ko wani abu.

Allah shine mafi sani

Leave a Reply

Scroll to Top