Hukuncin zuwa Wurin Bikin Aure ko Kamu

Mai Tambaya:Assalamualaikum Malam,, neighbors Ina sun gayyace mu bikin kamu Dani da mahaifiyata da kanwata amma na tsinci kaina da kokwanton naje ko karnaje. Kamun da ake yi yanzu Kadan ne ake samu masu bin tsarin musulincin Kuma bansan ya nasu zai Kasance ba.

Amsa:

Addinin Musulunci bai haramta zuwa wurin taro ba idan har ya zamto babu saɓon Allah a wurin. Amma idan har akwai tsaɓon Allah a wurin to baya halatta Musulmi yaje wannan Wuri.

Sannan Kuma shi Musulmi a kodayaushe ana so ya zamto mai taka tsan tsan game da lamarin Addinin sa, shiyasa Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya umar ce mu da mu kauce wa duk wani abinda akwai shubuha(Rikitar wa) acikin sa.

Shiyasa yace duk wanda ya nesan ce wa abubuwa masu rikitar wa to haƙiƙa ya nema wa kansa hanyar kuɓuta da Addinin sa, da Mutuncinsa.

Saboda haka wannan abu da kikayi bayani na cewa baki da Tabbas na cewa baza’a aikata abinda ya tsaɓa wa Shari’ar Muslunci ba kuma mafi yawancin irin wa’innan bukukuwa a wannan zamani namu baya kuɓuta daga saɓon Allah, ina Baki shawara ki zauna a gida kada kije shi yafi. Kada kije ki jefa kanki cikin saɓon Allah.

Amma idan ya zamto kin tambaya an tabbatar miki cewa zuwa kawai za’ayi a zauna a ci abinci a watse ba tare da aikata wani abu da tsaɓa wa Allah ba to wannan babu laifi kije.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top