Tambaya: Assalamualaikum malan tambayata shine Wanne mataki zanbi domin in haddace alqur’ani.
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Hanyoyin da Mutum zai bi domin haddace Alqur’ani suna da yawa. Amma dai ga wasu daga cikin shawarwari da zamu baka, muna sa ran in Sha Allah zai taimaka maka wurin yin Hadda. Muna roƙon Allah ya taimaka maka, ka samu ka cimma burin ka.
1. Ikhlasi(Yi domin Allah): Ya zamto ka ƙudurce a zuciyar ka cewa wannan hadda da kake so kayi zakayi shi domin Allah, ba domin ace ka iya ba ko kuma domin yin gasa ko burgewa ba, yin haka zai taimaka maka wurin samun yin haddan da kuma samun ladan sa. Domin babu lada ga wanda ya karanta Alqur’ani ko ya haddace domin riya.
2. Ka samu malami Makaranci: Shi Alqur’ani ba’a karantashi ba tare da Malami masani ba, domin Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam da kansa awurin Mala’ika Jibrilu yake karɓan Alqur’ani, haka nan sahabban sa sun karɓa daga wurinsa, haka lamarin yaci gaba da tafiya har ya iso zuwa wurin mu. Saboda haka baya halatta mutum ya buɗe Alqur’ani kawai yace zai koya da kansa, dole sai ya samu malami ƙwararre, domin kada yaje ya karantar dashi kuskure.
3. Ka ƙayyade iyakan Abinda zaka haddace kowani lokaci: duk lokacin da ka zauna hadda ka ƙayyade iya shafukan da kake so ka haddace, sai kayi ta maimaita su, kana rerawa da kyau, domin hakan zai taimaka maka wurin tabbatuwar haddar, kuma ka tabbatar kada ka wuce wa’innan shafukan har sai ka tabbatar ka haddace su sosai. Haka nan abinda zai taimaka maka wurin haddace Shafukan da ka ƙayyade kowani rana shine yawaita karanta su, da maimaita su acikin sallolin ka na nafila da na Farilla.
4. Yin amfani da bugun Alqur’ani kala ɗaya: Ya zamto kana amfani da bugun Alqur’ani kala ɗaya, domin hakan zai taimaka maka wurin haddace shafukan da kake karantawa. Kada ka rinƙa canza bugun Alqur’anin.
5. Fahimtar Ma’anar Ayoyin: Fahimtar ma’anar ayoyin Alqur’ani yana taimaka wa matuƙa wurin yin hadda, saboda haka yana da kyau bayan haddar ka haɗa da neman sanin ma’anonin ayoyin Surar da kake haddasce wa.
6. Kada ka wuce wata Surah har sai ka tabbata ta zauna: kada kayi gaggawa, kafin ka tsallaƙe wata sura ka shiga wata ka tabbata ta bayar ta zauna, domin idan ka wuce ta baya bata zauna ba to ta bayar zata rushe.
7. Ka samu mai ji maka haddar ka: ka samu wani wanda zai rinƙa ji maka Haddar ka, kada ka dogara akan muraja’ar ka kai kaɗai, ka samu lokaci zuwa Lokaci wani yana saurara maka, domin hakan na taimaka wa wurin gano kurkurai. Zaka iya amfani da manhajojin Muraja’a kamar na Qur’an Ai da makamantansu.
8. Yawaita Muraja’a: a kullum ya zamto akwai adadin shafuka da zakayi muraja’ar su, kada ya zamto kawai ƙari zaka tayi ba tare da karanta na baya ba. Domin shi Alqur’ani idan ba’a muraja’ar shi yana da saurin gudu. Kamar yadda Annabi ya bada labari.
9. Kula da Ayoyi masu kamanceceniya da juna masu rikitar wa: yayin da mutum yake hadda dole ya kula da ayoyi masu kamanceceniya da juna, ya kiyayesu ya san kowani Aya a wani Surah take. Hakan zai taimaka wurin tabbatuwar hadda da kauce wa kuskure.
10. Fara Hadda da wuri: Kada ka ɓata lokaci wurin fara haddar ka musamman idan kana da ƙarancin shekaru, domin hadda lokacin mutum na da ƙarancin shwkaru yafi zama a ƙwaƙwalwa.
Allah yasa mudace.