Hukuncin Shan wiwi

Tambaya: menene hukuncin shan wiwi? Wurin zuƙar hayaƙin sa ko kuma dafa shi a sha, Domin ance wiwi yana buɗe ƙwaƙwalwa.

Amsa: da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.

Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, lokacin da ya tura Mu’az bin Jabal da Abu Musa Al-Ash’ari zuwa Yamen, sai suka tambaye shi game da wani abin sha da akeyin sa a wannan ƙasa, wanda ake yin ɗayan da Zuma, ɗayan kuma da sha’ir.

Sai yace musu:

Duk wani abu mai bugar wa Haramun ne

Sahihul Bukhari: 4343

Wannan Hadisi ƙa’ida ce babba kan duk wani abinda mutum zai ci ko kuma zai sha.

Duk wani abinda mutum zai sha mai bugar wa to haramun ne, haka nan duk wani abinda mutum zai ci ko zai sha mai cutar wa shima haramun ne.

Domin Allah yace:

Yana halatta musu abubuwa masu daɗi tsarƙaƙa, kuma yana haramta musu abubuwa munana (Masu cutar wa).

Suratul Araf: 157

Saboda haka duk wani abu mai cutar wa, ko me bugar wa Haramun ne.

Abisa wannan dalilai da muka gabatar. Wiwi haramun ne a shashi ta kowacce hanya. Wasu maluman ma sunaga haramcin sa tafi ta giya.

An tambayi Maluma masu fatwa ta lajna game da hukuncin Wiwi Halal ne ko Haramun?

Sai suka ce:

Haramun ne sayan Wiwi, ko sayar dashi, ko Ta’amuli dashi. Wurin ci, ko sha ko taunawa. Saboda yana bugar wa, kuma yana cutar wa mai girma. Kuma hani yazo a shari’ar musulunci kan haramcin duk wani abu mai bugar wa. An rawaito a Sahih Muslim da Sunan Abi Dawud daga Ibnu Umar Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace “duk wani abu mai bugar wa giya ne, duk wani abu mai bugar wa haramun ne

Fatawa Lajnatudda’imah: 22/138

Shekhul Islam Ibnu Taimiyya yana daga cikin Maluman da suke ganin wiwi yafi giya muni, kuma za’ayi wa mai shan wiwi haddi irin na mai shan giya. Duba Siyasatush-Shar’iyya: 143.

Game da batun cewa wiwi yana buɗe ƙwaƙwalwa:

Shawara da zamu baiwa ɗan’uwa shine, babu wani alheri cikin dukkan abinda Allah ya haramta, koda ace da gaske ne wiwi na buɗe ƙwaƙwalwa, idan har Allah da manzon sa sun hana sha, to ya wajaba ga musulmi ya ƙaurace musu. Ballantana wannan magana babu tabbas akai, kuma idan akayi lura da amfanin da wiwi yake yi da kuma cutarwar sa zamu ga cutarwar tafi yawa. Saboda haka ka nesanci duk wani abinda Allah ya hana koda ko akwai wani amfani da zaka samu aciki, wannan shine hanya ta Muminai.

A taƙaice:

Shan duk wani abu mai bugar wa haramun ne, wannan ya shafi wiwi da ƙwaya da coccaine da sauran su. Kuma babu banbanci tsaƙanin mutum ya zuƙi hayaƙin, ko ya tauna, ko ya dafa ya sha.
ya wajaba akan musulmi ya guje wa duk wani abinda Allah ya hana.

Allah shine Mafi Sani.

Domin sanar damu wani kuskure danna nan

Leave a Reply

Scroll to Top