Haddin wanda ya sha giya a Shari’ar Musulunci

Tambaya: Menene haddin wanda ya sha giya a shari’ar Musulunci?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Haddin Wanda yasha giya shine bulala. Amma kuma Shari’a bata iyakance iya bulalar da za’ayi ba.

An rawaito daga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace:

Anzo da wani mutum wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam yasha giya, sai Annabi yace ku bige shi, Abu Huraira yace: daga cikinmu akwai mai dukansa da hannu, akwai mai dukansa da takalmi, akwai mai dukansa da tufan sa. Lokacin da aka gama dukansa ya tafi sai wasu daga Cikin sahabbai sukace: Allah ya wulaƙanta ka. sai Annabi yace: kada ku faɗi haka, kada ku taimaka wa shaiɗan akan ɗan’uwan ku.

Sahihul Bukhari: 6777

Wannan hadisi yana nuna cewa a lokacin Annabi babu wani adadi da aka ƙayyade na yin bulala ga wanda ya sha giya.

Shiyasa lokacin Abubakar Allah ya ƙara masa yarda sai ya sanya haddin wanda yasha giya bulala arba’in. A lokacin Umar aka samu mutane da yawa da suka shiga addinin Musulunci, aka samu yawaitar shan giya a lokacin sa, lokacin da ya ga haka sai ya nemi shawarar Sahabbai sai Abdurrahman Bin Auf Allah ya ƙara masa yarda ya bashi shawara da ayi amfani da mafi ƙarancin Haddi wanda shine bulala tamanin na mai ƙazafi. Sai Umar ya karɓi shawarar shi ya sanya haddin wanda yasha giya bulala tamanin.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top