Falalar ranar Arafa da Mafificin zikiri ranar

Tambaya: Wani zikiri ne yafi falala ranar Arafa?

Amsa: Ranar Arafa rana ce mai girma sosai, anaso Musulmi ya yawaita ayyuka na alheri acikin ta, ya azumci wannan rana, ya kuma yawaita Addu’a da ambaton Allah

An rawaito daga Uwar Muminai Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace; Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Babu wata rana da Allah yake yawaita ƴanta bayi daga wuta irin Ranar Arafa, Allah yana kusanto wa a wannan rana(kusantowa da ta dace dashi). Sai Allah yayi alfahari da bayinsa dake Arafa a gaban Mala’iku.

Sahih Muslim: 1348

Mafificin Zikiri a ranar Arafa: an rawaito daga Abdullahi bin Amru Bin Aas Allah ya ƙara masa yarda yace; Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Mafi alherin Addu’a itace Addu’ar ranar Arafa, mafi alherin abinda na faɗa da Annabawa kafin ni shine: “La’ilaha illallah, wahdahu la Sharika lahu, lahul mulku, wa lahul hamdu, wahuwa ala kulli shai’in Qadir”

Tirmidhi: 3585

Wannan Addu’a ya shafi Mai Hajji wanda yake Arafa da wanda bai je Hajji ba. Kowa zai iya wannan Zikirin.

Sannan kuma zai iya yin kowani irin addu’a na buƙatunsa a wannan rana. Domin rana ce da ake amsa Addu’oin bayi.

Leave a Reply

Scroll to Top