Hukuncin Cinikin Salam ko Salaf

Tambaya: Aslm.malam dafatan kana cikin koshin lafiya,ina maka fatan alkhairi , shin malam Yaya hukunci wannda yadau kudi misalin naira dubu 10,000 yaba manomi da yar” jejeniyan xai bashi masara awannan kudin bayan yayi nomanshi,malam shin wannan lamari ya halatta Ko ko aaa .malam Allah shikara maka imani da nisan kwana mai anfani ameen ya rabbi

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai

Akwai wani irin nau’i na kasuwanci a Shari’ar Muslunci da ake kiran sa Assalam ko Assalaf.

Wanda wannan nau’i na kasuwanci halal ne a Shari’ar Muslunci.

An rawaito daga Ibnu Abbas Allah ya ƙara masa yarda yace:

Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yazo garin Madina ya same su suna yin Ciniki na Salaf na dabino shekara biyu zuwa uku, sai yace: duk wanda zaiyi ciniki na Salaf acikin wani abu to yayi shi a adadi sananne, ko nauyi sananne sannan zuwa wani lokaci sananne.

Sahihul Bukhari: 2240,. Sahihu Muslim: 1604

Wannan Hadisin yana nuna halaccin ciniki na Salaf.

Misalin ciniki na Salaf shine:

Ka baiwa Mutum kuɗi naira 1,000 akan zai kawo maka mudun shinkafa ɗaya ranar biyar ga watan Shida shekara ta 2023. Kuma kun ƙulla kasuwancin ne a yau 14 ga watan Mayu 2023.

To irin wannan kasuwancin Halal ne.

Kuma shine irin kasuwancin da kayi tambaya akai.

Sai dai sharaɗin shine dole a san yawan kuɗin, da ranar da za’a kawo kayan, da kuma adadin kayan.

Amma baya halatta misali ka baiwa manomi kuɗi misali dubu goma amma ka kafa masa sharaɗi lokacin da zai baka kayan da ya noma zai ninka maka, saboda shi yana da buƙatar kuɗin a yanzu.

Amma idan kun shirya dashi zaka bashi kuɗi yanzu bayan ya nome ya baka iya adadin abinda kuka ƙulla yarjejeniya akai to babu laifi.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top