Hukuncin wanda ya samu kudi a Account da ya zo da layin da ya saya

Tambaaya:

Assalamu Alaikum tambayata shine
Mutum ne yaje yasayi sim card yayi register yake amfani dashi harkusan shekara kawaii sai yaga alart na kudi Kuma shi yasan bai bude account da wannan sim ba yai bincikensa Allah bai sa ya gano Mai wannan account ba har ya fara kokarin anfani da wannan kudin daga baya sai yagano ai kanfanin MTN ne idan sukaga andade ba a anfani da layi ne suke replace din sa.
To shin zai iya anfani da wannan kudin.

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Abune sananne a shari’ar Musulunci cewa baya Halatta ga mutum yayi amfani da abinda ba nashi ba sai idan an bashi izinin yin hakan

A bayanin da kayi idan na Fahimta ainahin mai layin na farko yana da Account da ya buɗe da wannan layin, daga bisani ya daina amfani da layin har MTN suka sabunta shi suka sayar maka, saboda haka wannan kuɗi da aka turo na ainahin mai layin da aka ƙulle ne.

Abinda ya dace kayi shine kaje bankin da aka turo kuɗin aciki kaje kayi musu bayanin abinda yake tafiya, suna da cikakken bayanin ainahin mai account ɗin, idan kuma ya mutu ne suna da bayanin address nashi ko magajin sa da ya rubuta awurinsu wanda daga nan zaka iya Samun ainahin mai kuɗin ko kuma ka samu magadan sa ka basu haƙƙin su.

Idan kuma kuskure ne akayi wurin turo kuɗin sai kayi jinkiri wanda ya turo kuɗin zai bibiyi kuɗin sa.

A kowani irin hali dai baya halatta mutum yaci wata dukiya wacce ba tashi ba, ko tsintuwa yayi dole sai ya nemi mai ita.

Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam yace:

Digadigan ɗan Adam bazasu gushe ba Ranar tashin Alƙiyama har sai an tambaye shi game da Dukiyar sa, ta ina ya same ta, sannan ta ina ya kashe.

Sahihut-Tirmidhi: 2417

Saboda haka ya wajaba ga Musulmi yayi taka tsantsan kan lamuran sa, ya tabbata dukiyar sa ya same su ne ta hanyar Halal, haka nan ya kashe su ta hanyar Halal.

A Taƙaice:

Baya halatta ka taɓa wannan dukiya, Kabi hanyoyi da ya dace wurin gano mai wannan kuɗi ka danƙa masa kuɗinsa.

Leave a Reply

Scroll to Top