Hukuncin cin Naman Doki da Jaki

Tambaya: Shin ya Hatalla aci naman doki? Ko jaki?

Amsa: mafi yawan malamai sun tafi kan halaccin cin naman doki, saboda hadisai ingatattu da sukazo kan halaccin hakan, haka nan Jakin daji Shima Halal ne aci. amma babu tsaɓani kan haramcin cin naman jakin gida.

An rawaito daga Jabir bin Abdullahi Allah ya ƙara masa yarda yace:

Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya hana cin naman Jakin gida, amma yayi rangwame game da Doki

Sahihul Bukhari: 3982. Sahihu Muslim: 1941

Haka nan Asma’u Bint Abi bakr Allah ya ƙara mata yarda tace:

Mun soke doki a zamanin Annabi Sallallahu alaihi wasalama Muka ci

Sahihul Bukhari: 5191. Sahihu Muslim: 1942

Haka nan an sake rawaito wa Daga Jabir Allah ya ƙara masa yarda yace:

Munyi tafiya da Annabi Sallallahu alaihi wasallama mun kasan ce muna cin naman doki, sannan muna shan nonon ta.

Daru Qutni: 4/288. AlbaihaQi: 19919

Da wannan Hadisan ne Maluma suka kafa hujja kan halaccin cin naman doki.

Amma wasu maluman suka ce Makruhi ne. Saboda Faɗin Allah acikin Suratun-Nahl Ayah ta: 8

Da doki, da alfadari, da Jaki, domin ku hau, da kuma ƙawa, Yana Halittar abinda ma baku sani ba.

Suratun-Nahl: 8

Wannan Ayah tana nuna cewa Allah ya Halicci Doki da Alfadari da jakin gida ne domin a hau, sannan ayi ado dasu, shiyasa sukace cin doki Makruhi ne.

Amma sai dai an basu amsa kan cewa ambaton hawa da ado acikin ayar ba yana nuna cewa iya abinda Allah ya halatta ayi da wa’innan nau’i na dabbobi ba kenan kawai. Ya ambaci hawa da ado ne domin shine mafi yawan abinda akeyi da wa’innan dabbobi.

A Taƙaice:

Naman Doki Halal ne, amma naman jakin gida Haramun ne. Babu laifi ga wanda yakeso yaci naman doki ko yasha nonon ta, amma kuma kada mutum ya ɗauka wata Sunnah ce cin naman doki. Itama Halal ce kamar sauran abubuwa da Allah ya halatta aci.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top