Rama Sallar da lokacin ta ya fita da Hukuncin Wasa da Sallah

Tambaya: Meye Hukuncin rama sallar da lokacin ta ya fita? da hukuncin mai jinkirta Sallah?

Amsa: Wanda baiyi Sallah ba har lokacin ta ya wuce idan yana da uzuri to zai rama wannan Sallar duk lokacin da wannan uzurin ya kau.

Misali mutum ya kwanta bacci baiyi sallar Azahar ba har sai Magrib kafin ya tashi, to anan zai sallaci Azahar, sannan La’asar sannan Magriba. Kuma babu wani laifi akansa idan har ba sakaci yayi ba.

An rawaito daga Anas bin Malik Allah ya ƙara masa yarda yace, Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Wanda ya mance Sallah, ko yayi bacci baiyi ba, kaffarar ta shine ya sallace ta idan ya tuna

Sahihu Muslim: 684

Amma idan mutum da gangan ya barta baiyi ba, bashi da wani uzuri, ya bari har lokacin sallar ta fita to an samu tsaɓani tsaƙanin Maluma shin zai rama ko bazai rama ba.

Magana ta farko: Itace magana ta Mazhaban nan guda huɗu, Hanafiyya, Malikiyya, Shafi’iyya, Hanabila. Dukan su sun tafi kan cewa wanda yayi sakaci baiyi Sallah ba har lokacin ta ya fita to yayi laifi mai girma amma kuma zai rama sallar.

Magana ta biyu: Wanda ya bar sallah har lokacin ta ya fita ba tare da wani uzuri ba to ba zai rama ba, Wannan Shine Mazhaba ta Zahiriyya, Sannan kuma shine zaɓi na Sheikhul Islam Ibnu Taimiyyah, da Ibnu Rajab, da Ibnu Baaz, da Ibnu Uthaymeen.

Sheikhul Islam Ibnu Taimiyyah yace:

Wanda ya bar Sallah da gangan Ba’a shar’an ta masa ramako ba, sannan koda ya rama baza’a karɓa ba. Abinda zaiyi shine ya yawaita nafilfili, da Azumi(domin neman Allah ya gafarta masa)

Alfatawal Kubra: 5/320

Masu wannan Magana ta ƙarshe sun kafa Hujja da Hadisai da Ayoyi, sannan sukace Sallah ibadah ce mai lokaci, ba’a yin ta kafin lokacin ta, to kamar yadda ba’a yin ta kafin lokacin ta to haka nan baya halatta ayi ta bayan lokacin ta sai dai idan akwai uzuri. Domin Allah yace:

Lallai Sallah ta kasance farilla ce mai ƙayyadadden lokaci.

Suratun-Nisa: 103

A taƙaice: Wasa da Sallah rashin yinsa acikin lokaci babban laifi ne, ya wajaba Akan Musulmi ya kiyaye lokutan Sallah ya rinƙa yinsu cikin Lokacin da Allah ya sanya musu.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top