Addu’ar sanya sabon kaya

Abu Sa’eed Al-khudri Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito idan Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yayi sabon tufa, sai ya ƙira shi da sunan shi, Riga ne ko rawani sai yace:

اللَّهمَّ لك الحمدُ أنت كسوْتنِيهِ أسألُك من خيرِه وخيرِ ما صُنِعَ له ، وأعوذُ بك من شرِّهِ وشرِّ ما صُنِعَ له

Allahumma lakalhamdu Anta kasautani hi, As’aluka min khairihi wa khairi ma suni’a lahu, wa A’uzu bika min Sharri hi, wa Sharri ma suni’a lahu

Sharhin Addu’ar: Ana so idan Musulmi ya sanya sabon tufa yayi wannan Addu’a. Ubangiji na dukkan yabo sun tabbata gare ka, kai ka tufatar dani wannan kaya, Ina roƙon ka daga alherin sa, da alherin abinda aka yishi domin shi, (ma’ana ya taimaka min wurin aikata aikin alheri cikin wannan kaya) Haka nan ina neman tsari daga Sharrin sa, da Sharrin Abinda akayi shi domin shi. (Ma’ana ka tsareni kada na aikata wani abinda yake tsaɓa maka ne dashi)

Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Scroll to Top