Girman matsayin Tauhidi da rabe raben sa da Girman laifin shirka

Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Mafi girman wajibi akan bayi shine Tauhidi (kaɗaita Allah).

Shirka shine laifin da Allah baya gafarta wa wanda ya mutu yana aikata shi.

Allah maɗaukakin sarki yace:

Lalle ne Allah baya gafarta a haɗa shi da wani, amma yana gafarta wani abu koma bayan haka ga wanda yaso, kuma lalle ne duk wanda ya haɗa Allah da wani to ya ɓata ɓata mai nisa

Suratun-Nisa: 116

Akwai ayoyi makamantan wannan da kuma hadisai da aka rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da suke nuni zuwa ga munin shirka.

Shiyasa Annabi tsira da Amincin Alla su tabbata a gare shi ya tsoratar da Abu Bakr Assiddik Allah ya yarda dashi yace masa:

Lalle shirka yafi ɓoyuwa fiye da tafiyar tururuwa

Sahihul Adabil Mufrad: 551

Kamar yadda tururuwa take tafiya babu mai jin takun ta, kuma ba’a iya ganin gurbin tafiyar ta, haka nan shirka yakan shiga aikin bayi ba tare da sun sani ba.

Saboda haka dole Musulmi ya zama mai taka tsan tsan kada ya faɗa shirka.

To wannan Tauhidi wanda shine da’awar Annaba wa baki ɗaya, kuma shine Annabi ya ɗauki shekaru goma sha uku a garin Makkah yana ƙiran mutane zuwa gare shi ya rabu kashi nawa?

Ansamu maluma da suka rarrabe Tauhidi zuwa rabe rabe mabanbanta, wasu daga cikin Maluma sun raba Tauhidi zuwa nau’uka uku.

  • Tauhidur-Rububiyyah
  • Tauhidul-Uluhiyya
  • Tauhidul Asma’i Wassifat

Sun samo dalilin wannan ne cikin faɗin Allah maɗaukakin sarki:

Ubangijin Sammai da ƙassai da abinda ke tsaƙanin su, ku bauta masa, kuma kuyi juriya wurin bautar sa, shin kasan wani takwara a gare shi?

Surat Maryam: 65

Wa’innan rabe rabe na tauhidi suna nuna cewa Allah shine mai halitta, mai raya wa mai kashe wa, sannan kuma shi ya cancanci a bauta masa shi kaɗai. Kuma bashi da wani wanda yake daidai dashi, yana sunaye kyawawa da sifofi masu kamala. Ana tabbatar masa da wa’innan sifofi yadda sukazo a nassi ba tare da anyi tawilin su ba

Wataƙila wani yayi tambaya yace:

To wani Ayah ne ko hadisi yazo da nassin wannan rabe rabe na tauhidi?

Amsa: kamar yadda idan mutum ya duba littafan Fiqhu zai ga maluma sun kawo farillan sallah, da sunnoni da mustahabbai da makamantan su, idan ka tambaya ina nassi da ya nuna wannan rabe rabe? Babu nassi da ya rarrabe haka ya ambaci adadin su. Amma maluman sun bibiyi nassin Alqur’ani da Hadisi ne suka fito da wannan Hukunce hukunce, shiyasa ma zaka ga ana samun tsaɓani tsaƙanin su kan adadin farillan sallah ko sunnonin sa da makamantan su.

To haka nan rabe raben Tauhidi shima sun bibiyi nassi ne suka fitar da wannan rabe rabe.

Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Scroll to Top