Wanda cire Zakkar Fidda kai ta wajaba a kansa

Tambaya: Shin wajibi ne ga Mahaifi ya cire wa ɗansa Zakkar fidda kai?

Amsa: Zakkar fidda kai zakka ce wajiba akan kowani Musulmi na miji ko mace, ƙarami ko babba, ɗa ko bawa. Kamar yadda Ibn Umar ya rawaito yace:

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya farlanta Zakkar fidda kai, Sa’i ɗaya na dabino, ko sa’i ɗaya na Sha’ir, akan bawa ko ɗa, na miji ko mace, ƙarami da babba daga cikin Musulmai, sannan yayi umarni a bada ita kafin mutane su fita zuwa sallar idi

Bukhari: 1503

Saboda haka wannan zakka wajiba ce akan wa’innan nau’ukan mutane da aka ambata.

Amma mahaifi zai cire wa ƴaƴan sa ƙananu, da wa’inda suke ƙarƙashin sa.

Idan kuma yaro ya girma yana da halin da zai cire wa kansa to shi zai cire wa kansa, ko kuma shi mahaifin bashi da halin cire wa, amma shi ƙaramin yaron yana da dukiya, to zai cire daga cikin dukiyar sa.

Allah shine Mafi Sani.

Domin sanar damu wani kuskure danna nan

Leave a Reply

Scroll to Top