Tambaya: menene hukuncin keɓance ranar Juma’a da yin azumi?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Babu laifi mutum yayi azumin nafila ranar Juma’a matuƙar dai ba ya keɓance ranar Juma’ar bane kawai, misali yayi azumi ranar alhamis da Juma’a, ko Asabar da Juma’a. Ko kuma ranar juma’ar ta dace da wani rana da akeso mutum ya azumta, kamar Ranar Arafah, ko kuma mutum ya saba azumi yau gobe ya huta, sai azuminsa ya dace da ranar juma’a, to nan ma babu laifi mutum yayi azumin sa.
Amma ƙeɓance ranar juma’a ita kaɗai domin yin azumin nafila baya halatta, saboda an rawaito Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana yin hakan.
Abu Hurairah Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
Kada ɗaya daga cikin ku ya azumci ranar Juma’a, sai dai idan zai azumci rana ɗaya kafin ta, ko rana ɗaya bayanta
Sahihul Bukhari: 1985. Sahih Muslim: 1144
An rawaito daga Juwairiyya Bint Alharith Allah ya ƙara mata yarda tace:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shigo wurin ta ranar Juma’a tana azumi, sai ya tambaye ta, shin kinyi azumi jiya? Sai tace A’a. Yace: Shin kinaso kiyi azumi gobe? Tace A’a. Sai yace to ki karya Azumin ki.
Sahihul Bukhari: 1850
Wa’innan hadisai guda biyu suna nuna cewa baya halatta a keɓance ranar Juma’a da azumi, sai dai idan za’ayi azumi kafin ranar ko bayan ranar.
Hukuncin Azumin Sitta shawwal ranar Juma’a
Shima Azumin sitta shawwal azumi ne na nafila, kuma lokacin sa na da faɗi, mutum zai iya yinsa duk lokacin da ya samu dama.
Amma idan mutum zaiyi azumin a jere ne ba tare da hutu ba to babu laifi ya azumci ranar juma’a idan ta dace da ranar azumin sa, domin zai tabbata cewa yayi azumi kafin ranar ko bayan ranar, wanda hakan babu hani akan sa.
Amma keɓance ranar Juma’a ita kaɗai da azumin Sitta shawwal baya halatta.
Ibhu Qudama yace:
Makruhi ne keɓance ranar Juma’a da azumi, sai dai idan ranar ta dace da ranar da yake azumin sa da ya saba, kaman wanda yake azumin kwana ɗaya, ya huta kwana ɗaya, sai azumin sa ya dace da ranar Juma’a, da wanda ya kasance Al’adar sa itace azumin farkon wata, ko ƙarshen ta, ko tsaƙiyan ta.
Almugni: 3/53
A taƙaice:
Allah shine Mafi Sani.
Domin sanar damu wani kuskure danna nan