Hukincin yin Sallar Janaza a lokutan da akan Hana sallah

Tambaya: Shin ya Halatta ayi Sallar Janaza a lokuta da aka hana Sallar Nafila?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Ibnu Abbas Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam

Annabi Ya hana Sallah bayan Sallar Asubahi har sai rana ta fito, haka nan bayan Sallar La’asar har sai rana ta faɗi

Sahihul Bukhari: 547. Sahihu Muslim: 1367

Wannan hadisi ya nuna ƙarara cewa baya Halatta Ayi sallar Nafila acikin wa’innan lokuta.

Amma sai dai Ramakon Sallah da kuma yin Nafila mai sababi halal ne ayi su a wannan lokuta. Haka nan Sallar Janaza.

Saboda Haka Nafilar da baya halatta ayi a wa’innan lokuta shine nafila wanda Mutum zaiyi ba tare da wani sababi ba. Amma kaman yin Tahiyyatul Masjid ya halatta ayi. Haka nan Ramakon Salloli na farilla ya halatta ayi a wannan lokuta.

Sai dai ana jinkirta sallar Janaza yayin da rana take fito wa har sai ta fito, haka nan yayin da Rana take zawali har sai tayi zawali, haka nan yayin da rana take faɗuwa har sai ta faɗi.

An rawaito daga Uqbah Bin Amir Allah ya ƙara masa yarda yace:

Lokuta guda uku Annabi ya kasance yana hanamu yin Sallah acikin su, haka nan yana hana mu binne mamatan mu acikin su.

1. Lokacin da rana ta fito har sai ta haura sama.

2. lokacin da rana ta kai tsaƙiya har sai ta karkata zuwa mafaɗan ta

3. Lokacin da Rana take shirin Faɗuwa.

Sahih Muslim: 831

A taƙaice:

Ya Halatta ayi Sallar Janaza bayan sallar asuba da la’asar, haka nan ya halatta ayi nafiloli masu sababi a wannan lokuta, kamar Tahiyyatul Masjid.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top