Tambaya: Yaushe ne aka haifi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi?
Amsa: Maluman Sirah ta tarihi sun samu tsaɓani kan tabbatar da rana da kuma wata da aka Haifi Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam, amma sun tabbatar da cewa an haife shi ranar litini, a shekarar giwa.
Imam Ibnul Qayyim Allah yayi masa rahama yace:
Babu tsaɓani kan cewa an haifi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ne a cikin garin Makka, sannan kuma an haife shi ne a shekarar giwa, an rawaito daga Ibnu Abbas Allah ya ƙara masa yarda yace: an haifi Annabi ne a shekarar Giwa. Wannan shine abin da babu shakka akansa.
Game da haihuwar sa rananr litini kuwa an rawaito daga Abu Qatada Alharith Bin Rib’iyyi Allah yayi masa Rahama an tambayi Annabi game da Azumin da yake yi ranar litini sai yace:
Wannan rana ce da aka haife ni aciki,
Sahihu Muslim: 1162
Saboda haka inda tsaɓanin yake shine watan da aka haife shi da kuma Rana ta nawa ne acikin watan.
Abinda ake da nassi a bayyane akai shine wanda mukayi bayani a sama, an haife Shi ne ranar Litini, a shekarar giwa.
Zai dace da shekara ta 53 kafin Hijira, Miladiyya 571 kenan.
Allah shine mafi sani