Tambaya: Menene Hukuncin tashiwa tsaye domin girmama Shugaba ko wanin sa, ko kuma tsayuwa a bayan sa domin girmama shi.
Amsa: Tashiwa ko tsayuwa ya rabu kaman haka:
1. Na ɗaya: A tashi a tsaya a bayan mutumin da ake girmama wa shi yana zaune, ba dun ana tsoron za’a kawo masa farmaki ba, Wannan baya halatta, Saboda ba’a rawaito Annabi yana sanya wasu daga cikin Sahabban sa suna tsaya wa a bayan sa ba, wannan Al’ada ce ta wa’inda ba Musulmai ba. Shiyasa lokacin da Annabi baya jin daɗi yayi sallah a zaune ya umarci Sahabban sa suma su zauna.
2. Na Biyu: A tashi a tsaya wa wani saboda girmamawa yayin shigan sa ko fitan sa, wannan Shima bashi da kyau. Domin Annabi yayi umarni idan Mutum ya haɗu da ɗan ‘uwan sa Sallama zasu yi suyi Musafaha. Sannan ba’a rawaito Sahabban Annabi suna tashi masa ba.
3. Na Uku: A tashi domin tarbar wanda yazo, azo a gaida shi ayi musafaha. Wannan babu laifi. Bal ma Sunnah ce. domin Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam da kansa ya tashi ya tarbi ƴar sa Faɗima Allah ya ƙara mata yarda. Haka nan Annabi ya umarci Sahabbai su tashi wa Sa’ad bin Mu’az lokacin da yazo domin yayi Hukunci kan Bani ƙuraiza.
Allah shine mafi sani.