Tambaya: Shin ya Halatta Mahaifi ya Tirsasa ƴar sa ta auri wani da yake masa ganin Mutumin kirki ne?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Baya halatta ga Mahaifi ko majiɓincin Lamarin mace ya aura mata Mijin da bata so, kamar yadda shima na Miji baya halatta a tirsasa masa ya auri wacce baya so.
Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam yace:
Ba’a aurar da Bazawara har sai an nemi shawaran ta, ba’a aurar da Budurwa har sai an nemi izinin ta,
Sahihul Bukhari: 5136
Wannan hadisi ya nuna cewa Mace ba’a yi mata auren dole, sai da izinin ta kafin a aura mata wani.
Abinda ya dace idan mahaifin ya ga wani mutumin kirki da ya dace ta aura, sai ya zaunar da ita ya bata shawara kan ta aure shi.
Haka na a ƙissar Barira da Mijin ta, da Annabi ya nemi ta koma zuwa wurin mijin ta mugith, sai tace wa Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Shin kana umar ta ta ne in koma? Sai yace A’a ina nema masa ceto ne. Sai tace to bata da buƙatar sa.
Anan Annabi bai tirsasata ta koma ba duk da yana da ikon hakan.
A Taƙaice:
Allah shine mafi sani