Hukuncin Magana yayin karanta AlQur’ani

Tambaya: Shin ya halatta mutum yayi magana yayin karanta Alƙur’ani? Misali yana cikin karatu sai wani yayi masa magana ya halatta ya Amsa?

Amsa: da sunan Allah mai rahama mai ji kai

An Tambayi Sheikh Bin Baz Allah yayi Masa Rahama irin wannan Tambaya, ga Amsar da ya bayar a taƙaice:

Yace:

Bamu san wani damuwa ba game da haka, bamu san akwai wani laifi game da mutum yayi magana yana karatu ba; sai dai ya shagaltu da karatun sa kada ya shagaltu da magana shi yafi dace wa, hakan zai bashi dama wurin yin Tadabburin(Lura) da abinda yake karantawa, da hankaltar sa, hakan shi yafi falala idan har babu wata buƙatar da zaisa mutum yayi magana, amma idan akwai wata buƙata da zata sanya mutum yayi magana to babu laifi. Yayi maganar sa sannan yaci gaba da karatun sa, Misali wani yayi masa sallama babu laifi ya amsa sai yaci gaba da karatun sa, ko yaji mai kiran Sallah, zai dakatar da karatun ya bi kiran Sallar in ya kammala sai ya koma karatun sa. Duka wannan babu laifi akai, amma magana wanda ba’a buƙatar ta bata dacewa ga mai karanta Alƙur’ani ya shagaltu da ita. abinda yafi dacewa shine mutum ya shagaltu da karatun sa, domin ya samu daman Yin Lura da Abinda yake karantawa wanda shine abinda ake nema daga mai kararun Alƙur’ani.

Allah maɗaukakin Sarki yace:

Wannan Littafi ne wanda muka sauƙar zuwa gareka, domin suyi lura da Ayoyin sa, sannan masu hankali su riƙa yin tunani

Suratu Sad: 29

A Taƙaice:

Babu laifi ga mai karatun Alƙur’ani yayi magana idan har akwai buƙatar hakan, amma bai dace a gareshi ba ya shagaltu da Magana mara amfani yayin karatun sa.

Allah shine Mafi sani.

Domin sanar damu wani kuskure ku tuntuɓe mu ta WhatsApp

Leave a Reply

Scroll to Top