Tambaya: Menene Hukuncin neman auren mace kafin ta kammala idda? Shin idan mutum ya nemi auren ta kafin ta kammala iddar ta da rashin sani ya halatta suyi aure bayan ta kammala?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Baya halatta mutum ya nemi auren mace a yayin iddar ta da kalma bayananne wanda yake nuna neman aure har sai ta kammala.
Kamar mutum yace idan kika kammala idda inaso na aure ki, ko kuma yaje ya nemi auren ta a wurin waliyyin ta. duka wannan baya halatta.
Amma yin nuni ba tare da bayyana wa a fili ba ya halatta.
Misali kaman yace mata ina neman mata in aura, ko kuma yace duk wani namiji zaiso ki kasance matar sa. da makamantan wannan, wanda maganar bata ƙunshe da kalma wanda ke nuni da cewa yana neman auren ta a fili.
Wannan shine abinda Allah yayi bayani akansa acikin Suratul Baqara ayah ta 235.
Babu laifi ga na miji ya nuna yana son auren mace matuƙar ba da kalmar da yake nuna neman auren a fili bane, sannan kuma ya zamto macen da zai nuna yana son auren tan, mijin ta ya mutu ne ko kuma rabuwa ce wanda babu kome.
Amma wanda mijin ta ya sake ta saki ɗaya, ko biyu baya halatta mutum ya nuna yana sonta da aure, domin haryanzu tana matsayin matar aure ce.
Saboda haka Haramun ne Mutum ya nemi auren mace yayin iddar ta, kuma idan aka ɗaura aure a wannan yanayi to auren bai yi ba.
Shin idan mutum ya nemi auren ta kafin ta kammala iddar ta ya halatta suyi aure bayan ta kammala iddar?
Kamar yadda mukayi bayani a baya, baya halatta a nemi auren mace mai idda sai dai idan nuni mutum zaiyi da cewa yanaso ya aure ta ba tare da ya furta lafazi da ke nuna neman aure ba.
Saboda haka idan mutum ya nemi auren mace acikin iddar ta da sanin sa to yayi laifi mai girma, amma hakan bazai haramta masa ita ba bayan ta kammala idda.
Sai dai ya tuba ya koma zuwa ga Allah, ya nemi gafarar abinda ya aikata na laifi. itama ta tuba ta koma zuwa ga Allah.
Amma ya halatta ya aure ta bayan ta kammala iddar ta.
A taƙaice:
Allah shine Mafi Sani.
Domin sanar damu wani kuskure danna nan