Tambaya: Bazawara ce akayimata aure amma bataso saboda biyayya ga iyaye ta amince, sedai kuma sharrin shedan yaja da wanƙsnan auran Nata take soyayya da tsohon saurayinta ta waya harma Yana turo mata kuɗi tanayin buƙatunta amma shi baisan tayi aure ba, Haka suka cigaba da soyyaiya shi baisan tayi aure ba daga karshe dai auran Nata ya mutu sannan ta tuba sosai tayi nadama da abinda ta aikata.
Tambayar itace shin ya halatta ta aure wanan saurayin Nata da tayi soyyaiya dashi da auran ta koko babu aure tsakaninsu?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Da farko Addinin Musulunci ya hana auren dole, kamar yadda mukayi bayani cikakke kan hukuncin auren dole a wannan Fatawa da muka bayar, saboda haka iyayen ki sunyi kuskure babba wurin aura miki wanda baki so.
Sannan duk da haka kema kinyi babban laifi ta yadda kika ci amanar mijin ki wurin yin Mu’amala da wani namiji a waje alhali kina da aure. Wannan babban laifi ne, Dole ki tuba ki koma zuwa ga Allah ki nemi gafarar sa kan wannan abu da kika aikata.
Game da Tambayar ki: Shin ya halatta ki auri wannan saurayi da kukayi alaƙa dashi alhali lokacin kina da miji?
Babu wani dalili a Shari’ah da zai hana aure a tsaƙanin ku. Domin wannan laifi ne kuka aikata, wanda kuma wannan laifi bai haramta ki a gare shi ba.
Saboda haka idan har kun samu fahimtar juna babu laifi kuyi aure a tsaƙanin ku.
Abu mai mahimmanci shine ku tuba, tuba mai kyawu ta yadda bazaku sake komawa zuwa ga aikata wannan mummunan aiki ba har abada.