Tambaya: Shin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya taɓa karanta Suratul Baqara acikin Sallah ta farilla?
Amsa: dasunan Allah mai Rahama mai jin ƙai
Sallar Farilla ta Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ta kasance tsaƙa tsaƙiya, baya tsawaita wa sosai, sannan kuma baya gajarta shi sosai idan yana Sallah tare da mutane.
Ya kan karanta surori tsaƙanin Suratul Hujurat zuwa Abasa a Sallar asuba, da Azahar
A sallar isha’i kuma yakan karanta surori tsaƙanin Abasa zuwa Duha.
A sallar la’asar da Magriba kuma yakan karanta surori tsaƙanin suratu Dhuha zuwa Nasi.
Amma salloli na farilla Annabi yana karanta abinda ya tsawwaƙa aciki, amma yana tsawaita karatu acikin nafilolin dare.
Amma bamu tsaƴa kan wata riwaya da take nuna cewa Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya taɓa karanta Suratul Baqara dukkansa acikin Sallah ta farilla sai dai nafila. Domin hakan ta tsaɓa wa karantar sa.
Huzaifa Bin Yaman Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito yace:
Wata rana nayi sallar dare tare da Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, Annabi ya buɗe Suratul Baqara ya fara karanta wa, sai nace zaiyi ruku’i idan ya cika ayoyi ɗari, sai ya wuce, sai nace zai karance ta acikin Raka’a ɗaya, sai ya karance ta ya buɗe Suratun-Nisa ya karance ta, ya buɗe Suratu Aal Emran ya karance ta, yana karatu a natse a tsanaƙe, idan ya wuce ayah da take umarni da Tasbihi sai yayi tasbihi, idan ya wuce ayar roƙo sai ya roƙa, idan ya wuce ayar neman tsari sai ya nemi tsari, sannan sai yayi ruku’i, yana faɗin “Subhana Rabbiyal Azim” acikin ruku’in sa, Tsawon Ruku’in sa kaman tsayuwan sa, sannan ya ɗaga kansa yace “Sami’a-Llahu liman hamidahu” tsawon tsayuwar sa kaman Ruku’insa, sannan yayi sujada, tsawon sujadar sa kaman tsayuwan sa.
Sahih Muslim: 772
Wannan hadisi akwai abubuwa da dama da zamu ɗauka aciki, kaɗan daga cikinsu:
1. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsawaita wa a sallar nafilar dare.
2. Idan mutum yana karatun sallar nafila babu laifi idan ya wuce da ayar tasbihi yayi tasbihi, idan ya wuce ayoyi na addu’a ko neman tsari ya roƙi Allah dasu.
3. Ba dole idan mutum na karatun Sallah sai ya karanta surori a jere ba, domin Annabi ya fara karanta Suratun-Nisa’i sannan Aal Emran.
Wannan game da nafila kenan, amma game da sallar farilla munyi bayani a baya cewa Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana yin sa ne tsaƙa tsaƙiya, baya tsananta wa, yayi ma hani da tsananta wa yayin jagorantar mutane a sallah.
Abu Mas’ud Uƙbat bin Amru Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito:
Wani mutum yazo wurin Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace ya Manzon Allah, lallai ni ina jinkirin zuwa Sallar Asubahi saboda wane, saboda tsawaita wa da yake yi acikin Sallah, mai riwayar hadisin yace: ban taɓa ganin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yayi fushi cikin wa’azin sa ba irin yadda yayi a wannan rana, sannan yace: “Ya ku Mutane, daga cikin ku akwai masu kore mutane, duk wanda zai jagoranci mutane sallah to ya taƙaita, domin acikin masu binshi akwai manya masu shekaru, da masu rauni, da kuma mabuƙata.”
Bukhari: 7159. Muslim: 466
Wannan hadisi yana nuna tsawaita wa a sallar farilla idan mutum yana jagorantar mutane sallah tsaɓanin Sunnar Annabi ne, idan liman zai jagoranci mutane sallah to ya tuna a bayan shi akwai tsoffi, da Masu rauni, da wasu masu buƙata ta daban, sai yayi sallar ba tare da tsanantawa ba.
Saboda haka abinda yafi dace wa shine musulmi yayi koyi da sunnar Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, kada ya wuce inda Annabi ya tsaya. Amma idan shi kaɗai yake yin sallah a gida to ya tsawaita yadda yaso babu laifi, amma idan yana jagorantar mutane sallah to sunnah shine ya taƙaita.
Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya Allah yayi masa rahama yace:
Abinda yafi falala ga limami shine yayi koyi da Sallar Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda yake yi tare da sahabban sa, wannan Shine abinda yake a shari’a wanda Annabi yake umartan limamai dashi kamar yadda ya Umarci Malik Bin Huwairith da Abokin sa yace musu “idan Lokacin sallah yayi kuyi ƙiran sallah, ku tada Sallah, a samu ɗaya daga cikin ku ya jagorance ku, sannan kuyi Sallah kamar yadda kuka ga nake yi
Majmu’u fatawa: 22/318
A taƙaice
Allah shine mafi sani.
Domin sanar damu wani kuskure danna nan