Tambaya: Menene hukuncin jini da yake fita wa mace wanda ba na Al’ada ba?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Mace mai jini na ciwo tana da yanayi guda uku.
Na farko:
wacce ta san ranaku da lokacin zuwan jinin Al’adan ta, to wannan zatayi amfani da wa’innan ranaku da kuma lokacin da yake zuwa.
Misali:
Mace ce ta kasance ko wani wata Al’adan ta yana zuwa mata ne a farkon wata, kuma yana zuwa ne na kwanaki biyar kacal. To anan idan aka samu jini na ciwo yazo mata zatayi amfani da wa’innan kwanakin ne, da kuma lokaci. Da zarar kwanakin sun wuce zata yi wanka, sannan kuma taci gaba Ibadun ta.
Na Biyu:
Wacce bata san kwanakin jinin Al’adan ta da lokacin da yake zuwa ba, kamar wacce ta fara yin Al’ada sabo kenan. To wannan zata rabe tsaƙanin Jinin Al’ada ne da na ciwo da abinda ya bayyana mata na kalan Jinin da warin sa. Domin jinin Al’ada da na ciwo akwai bambanci a tsaƙanin su, shi na Al’ada yana zuwa da kauri, sannan kuma baƙi ne, kuma yakan zo da wari. To idan mace zata iya banbance tsaƙanin jinin ciwo da na Al’ada to da zarar ta samu tabbacin cewa jinin da yake fitan nan jini ne na ciwo to zata yi wanka sannan kuma taci gaba da Ibadun ta.
Misali:
Mace a farkon jinin ta, ta ganshi yana zuwa baƙi, da kauri, sai yaci gaba da zuwa har kwanaki goma ko fiye da haka, amma bayan kwanaki goma sai kalan jinin ya koma ja, kuma siriri, to daga wannan lokaci zata yi wanka ta fara ayyukan ta na Ibada. Domin jinin da yazo na ƙarshe jini ne na Ciwo ba na Al’ada ba.
Na Uku:
Macen da bata san kwanakin Jinin Al’adan ta ba, da kuma lokacin da yake zuwa, sannan kuma bata iya banbance tsaƙanin jinin da yake zuwa mata, bata iya rabe tsaƙanin na Al’ada da wanda ba na Al’ada ba, ko kuma yana rikitar da ita. To wannan zata yi amfani da kwanakin mafi yawan Mata irin ta sai Jinin Al’adan ta ya kasance kwanaki shida ko bakwai gwargwadon yadda taga yafi kwanta mata a rai, da kuma yadda yafi dace wa da mataye irin ta, wurin shekaru da Halitta. idan yaci gaba da zuwa ya wuce kwanaki shida ko bakwai to zata yi wanka taci gaba da ibadunta domin Wannan jini da yaci gaba da zuwa ɗinnan zata lissafa shi a matsayin jini ne na Ciwo(Istihada)
Misali:
Mace ce ta fara jinin Al’ada kenan bata san kwanakin ta ba, sai jini yaci gab da zuwa bai yanke ba, kuma kalan jinin ɗaya ne bai canza ba. To a nan zata yi amfani da kwanki shida ko bakwai, da zarar jini yaci gaba da zuwa ya wuce wannan kwanaki to zata yi wanka sannan kuma taci gaba da ibadun ta.
Hukuncin Mace mai jini na ciwo( Istihada)
Idan mace ta tabbatar da jinin da yake fita mata ba jini ne na Al’ada ba to hukuncin ta hukunci ne na mace mai tsarƙi. Duk wani Hukunci na Shari’ah ya hau kanta, zatayi sallah Azumi da duk sauran Ibadu baki ɗaya, kuma mijin ta zai iya kusantar ta a bisa magana mafi inganci.
Sai dai akwai wasu abubuwa da ya keɓanta ga mace mai jinin ciwo ( istihada) gasu jamr haka:
1. Ya wajaba a gareta tayi alwala ga kowani Sallah da zatayi.
2. Idan tazo yin alwala to zata wanke gurbin jini da ke farjin ta, kuma tayi amfani da auduga ko tsumma wurin katse shi.
Koda ta fara Sallah sai jini ya zubo mata wannan babu komi a kanta.
Wannan Hukunci da muka kawo a sama dalilan su shine hadisai da aka rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi
An rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:
Faɗimatu ƴar Abi hubaish tazo wurin Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi tace “Ya Manzon Allah, ni mace ce wacce jini na ciwo yake zuwa mata, bana tsarƙaƙa, shin zan bar yin Sallah?” Sai yace: “A’a, ai wannan ciwo ne ba jinin Al’ada bane, idan jinin Al’adan ki yazo to ki bar yin Sallah, idan kuma ya tafi to sai ki wanke jinin (na jinin ciwon) sannan sai kiyi Sallah”
Bukhari: 228. Muslim: 333
Wannan Hadisi ya nuna mana cewa Jinin ciwo (istihada) baya ɗaukan hukuncin jinin Al’ada, saboda haka mai jinin ciwo zatayi dukkan Ibadun ta, Kawai abinda zatayi shine zata rinƙa sabunta alwalanta ga kowani Sallah, Sannan kuma zata wanke jinin da ke jikin ta kafin tayi Sallah.
Sannan Hadisi na biyu shine Hadisin Hamnatu bint jahsh.
Tazo ta tambayi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da Jini da yake zuwa mata wanda ba jinin Al’ada bane sai ya umarce ta ta rinƙa lissafa kwanaki shida ko bakwai sune kwanakin jinin Al’adan ta a kowani wata, sannan sauran kwanakin kuma zata cigaba da ayyukan ta na Ibada.
Abu Dawud: 287. Tirmidhi: 128
A taƙaice
Allah shine mafi sani.
Domin sanar damu wani kuskure danna nan