Tambaya: Menene Hukuncin Shan Rubutu?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Shan Rubutu ya rabu kashi biyu, akwai rubutu wanda ya ƙunshi ayoyin Alƙur’ani ko Addu’oi da aka rawaito daga Annabi Sallallahu Alaihi wasallama, to wannan babu laifi a karanta a tofa wa mutum idan yana fama da wani rashin lafiya ko domin neman tsari, hakanan za’a iya rubuta wa asha babu laifi yin hakan saboda dalilai da zamu kawo nan gaba.
Kashi na biyun shine rubutu wanda ake rubuta wasu hatimai ko wasu abubuwa wanda ba’a san ma’anar su ba, kamar yadda Yan tsubbu sukeyi to wannan baya halatta mutum yasha.
Imam Ibnul Qayyim ya kawo acikin Littafin sa “Zadul Ma’ad” game da Ruƙiyya da za’ayi wa wanda ya samu kambun Baka. Yace:
Wasu Jama’a daga cikin magabata suna ga a rubuta masa ayoyi na Alqur’ani mai Girma, sannan yasha. Mujahid yace: babu laifi a rubuta ayoyin AlQur’ani a wanke a baiwa mara lafiya yasha. Sannan an ambata daga Ibnu Abbas cewa yayi umarni a rubuta ayoyin Alqur’ani wa wata mata da haihuwa yayi mata wahala sai a wanke a bata tasha. Abu Ayyuba yace: naga Abu Qilaba ya rubuta wani abu na Alqur’ani sannan ya wanke shi da ruwa ya shayar dashi wani mutum wanda yake fama da wani ciwo.Zadul Ma’ad: 4/170
Haka nan masu Bada Fatawa ta Lajnatudda’imah sun bada Fatawar Halaccin Rubuta ayoyin Alqur’ani da kuma shan su. A duba fatawa lajnatudda’imah: 1/97
Hakan Nan wannan itace Fatawar Ibnu Baz Allah yayi masa Rahama. Rubuta Ayar Alqur’ani da Shan sa domin neman waraka wannan Babu laifi. Fatawa Islamiyya: 1/30
A Taƙaice:
Ya halatta a sha rubutu dake ƙunshe da Ayoyin Alqur’ani mai girma, ko Hadisan Annabi, Amma baya Halatta Shan Wasu abubuwa da ba’asan asalin su ba. Kaman Hatimai da Makamantan su.
Allah shine Mafi Sani. Idan akwai wani Kuskure zaku iya danna nan domin tuntuɓar mu.