Tambaya: meye hukuncin tallata ɗakunan hotel?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Gina hotel da yin aiki a hotel asalin sa halal ne, sai dai idan akwai abubuwa da suka tsaɓa wa shari’a da ake aikata wa aciki to anan baya halatta musulmi ya taimaka wa masu aikata laifi.
Allah maɗaukakin Sarki yace:
Kuma ku taimaki juna kan aikin ƙwarai da tsoron Allah, kuma kada ku taimaki juna kan Laifi da ƙetare iyaka(Zalunci)
Suratul Ma’idah: 2
A ƙarƙashin wannan Ayah duk wani abu da yake na bin Allah ne, mutum zai taimaka wurin yin sa, duk wani abu na tsaɓon Allah kuma mutum bazai taimaka a aikata ba.
Saboda haka idan ya zamto wannan hotel ɗin masu shi suna tsare dokokin Allah, basu bari a aikata alfasha aciki, ko asha giya, ko a aikata duk wani nau’uka na tsaɓon Allah iya gwargwado suna kiyaye wa to ya Halatta musulmi yayi aiki a wannan hotel ɗin, ko ya tallata shi.
Amma idan ya zamto hotel ɗin ana aikata alfasha aciki, ana saɓon Allah to baya Halatta Musulmi yayi aiki a wurin ko ya tallata shi.
An Tambayi Maluma na Lajnatudda’imah ta Fatwa game da mutumin da yake aiki a gidaje da ɗakuna, kuma yana ganin abubuwa da ake aikata wa wanda yake fusata Allah, ta yadda akeyin liwaɗi, zina, shan giya, da chacha acikin su, kuma meye hukuncin Albashi da yake karba na wannan aiki?
Sai suka Amsa suka ce:
Baya halatta a gare ka kayi aiki awurin wanda yake bada hayan gidaje da ɗakuna wanda ake aikata saɓon Allah da munanan ayyuka aciki, domin wannan yana daga cikin taimakekeniya akan Laifi da ƙetare iyaka. Abinda kake karɓa na albashi na wannan aiki Haramun ne, domin lada ne na aikin Haram, ka nemi arziƙi a hanya da ta dace, acikin halal akwai abinda zai wadatar da mutum ga barin Haram. Allah maɗaukakin sarki yace: “duk wanda yaji tsoron Allah, Allah zai samar masa da mafita, kuma zai azurta shi ta yadda baya zato” Surat Talaq: 2-3
Fatawa Lajnatud-da’imah: 15/110
A taƙaice:
Allah shine Mafi Sani.
Domin sanar damu wani kuskure danna nan