Baya Halatta Musulmi ya ƙaurace wa ɗan’uwansa fiye da kwana uku

Tambaya:Aslm Malam shin mai y kamata mutum yayi a musulunce in Dan uwan sa yace we should not be talking to each other?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Da Farko ya kamata ka sani cewa Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne, koda Ƴan’uwantaka ta jini bata haɗasu ba, kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya hana ƙiyayya tsaƙanin Musulmi da ɗan’uwan sa.

Anas bin Malik ya rawaito Hadisi daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Kada kuyi ƙiyayya da juna, kada kuyi hassada da Juna, kada ku juya wa juna baya, ku kasance bayin Allah ƴan’uwa, baya halatta ga Musulmi ya ƙaurace wa ɗan’uwansa fiye da kwana uku

Sahihul Bukhari: 6065, Sahihu Muslim: 2559

Wannan Hadisi yana nuna mana muhimmancin ƴan’uwantaka a Musulunci, da hani kan ƙiyayya tsaƙanin Musulmai.

Saboda haka wannan abinda wannan ɗan’uwan ka ya faɗa maka ba daidai bane, sai ka sanar dashi cewa hakan baya Halatta, idan yaƙi idan ka haɗu dashi kai kayi masa Sallama, idan bai amsa ba ka samu ladan ka, shikuma laifi na kansa, kuma Allah zai ƙara maka ɗaukaka.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Scroll to Top