Mustahabbi ne tafiya Masallacin Idi da ƙafa

Tambaya: Meye Falalar tafiya Masallacin idi da ƙafa?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Mustahabbi ne zuwa Masallaci a ƙafa, na Idi da waninsa. Saboda hadisai da suke nuna falalar takawa zuwa Masallaci.

Wannan Shine abinda Maluman Mazhabar Musulunci guda huɗu suka yi ittifaƙi akai.

Sannan an rawaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam yace:

Idan aka kira Sallah, kuje kuna tafiya da ƙafa.

Bukhari: 908. Muslim: 602

Wannan hadisi Umuminsa yana nuna Mustahabbancin zuwa Masallaci da ƙafa, domin Sallar idi ko wanin sa.

Leave a Reply

Scroll to Top